Yayin da Rikici Ya Barke a ADC, INEC Ta Kara Wa'adin Sa Sunayen 'Yan Takara
- APC da PDP sun kammala shigar da sunayen 'yan takarar su a shafin INEC kafin ƙarewar wa'adin farko na 11 ga Yuli 2026
- INEC ta kara lokacin da duk jam'iyyun siyasa za su shigar sunayen 'yan takarar su har zuwa ranar Talata 14 ga Yuli 2026
- APC ta yi wa jam'iyyun adawa dariya bayan sun kasa daura sunayen 'yan takara a kan lokaci, tana cewa hakan ya nuna rashin shirinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Hukumar Zaben Najeriya (INEC) ta yi wa jam'iyyun siyasa ƙarin kwana uku don daura sunayen 'yan takarar su ashafin shigar bayanan 'yan takara na hukumar.
Sanarwar ta zo ne daga Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin Tattara Bayanan Jama'a da Ilmantar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna.

Source: Twitter
Dalilin kara wa'adin INEC
A sakon da ta wallafa a X, INEC ta ce ta yanke shawara ne bayan majalisar IPAC ta kawo buƙatar haka a madadin jam'iyyun da suka kasa cika wa'adin a lokacin da aka ƙayyade.
Rahotanni sun nuna cewa sabon wa'adin da hukumar INEC ta ba dukkan jam'iyyun siyasa zai ƙare da tsakar dare ranar Talata, 14 ga Yuli 2026.
APDP da APC sun kammala
Shugaba AnPC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar cewa jam'iyyar ta shigar da sunayen 'yan takara 471 gaba ɗaya, ciki har da 'yan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa, 'yan takarar sanata 109, da 'yan takarar majalisar wakilai 360.
Yilwatda ya nuna farin ciki da cewa APC ta cimma wannan mataki kuma yanzu za a mayar da hankali wajen gangamin zaɓe.
A gefen PDP kuwa, shugaban jam'iyyar, Abdulrahman Mohammed ya sanar cewa an shigar da sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa da kuma 'yan takarar majalisar tarayya.
Rahoton Punch ya nuna cewa ministar babban birnin tarayya Nyesom Wike ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar a wannan matakin.
APC da yi wa 'yan adawa dariya
APC ta yi amfani da damar yiwa jam'iyyun adawa dariya, inda Felix Morka ya fitar da sanarwa yana mai cewa rashin cika buƙatar INEC a kan lokaci ya nuna ƙarancin tsarin gudanarwa na jam'iyyun adawa.
APC ta ce hakan ya ƙara tabbatar da rashin ikon jam'iyyun adawa na sarrafa harkokin cikin gida, musamman idan aka yi la'akari da cewa APC na da 'yan takara fiye da su.

Source: Facebook
INEC ta yi kira ga duk jam'iyyun siyasa da su yi amfani da ƙarin lokacin wajen kammala aikin shigar sunayen 'yan takarar su kafin lokacin ya ƙare.
ADC ta sa sunayen 'yan takara
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsagin Nafiu Bala na jam'iyyar ADC sun sanar da cewa sun kammala daura sunayen 'yan takara.
Nafiu Bala ne ya fitar da sanarwar cewa sun sanya bayanan 'yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa da za su wakilci ADC a zaben 2027.
Sanarwar da tsagin jam'iyyar ya fitar ya tayar da kura lura da cewa wasu na tsammanin bangaren su Atiku Abubakar ne zai sanya sunayen 'yan takara.
Asali: Legit.ng

