APC Ta Taɓa Sunaye kafin Mika wa INEC Jerin ‘Yan Takara a Zaben 2027

APC Ta Taɓa Sunaye kafin Mika wa INEC Jerin ‘Yan Takara a Zaben 2027

  • Jam’iyyar APC ta mika fam ga wadanda za su yi takarar Majalisar wakilan tarayya da na Majalisar dattawa a zaben 2027
  • Ana zargin cewa an canza wasu sunayen ‘yan takara makonni kadan bayan an bada tikiti ta zaben tsaida gwani ko maslaha
  • Duk wanda APC ta damka wa wani fam da ake kira EC9 shi ne zai yi takara da zarar sunansa ya shiga shafin hukumar INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jam’iyyar APC ta soma daura sunayen wadanda za su yi mata takarar Majalisar wakilai da Majalisar dattawa a shafin hukumar INEC.

Hakan yana zuwa ne bayan zaben tsaida gwani da kuma tsarin maslaha da aka bi wajen fito da ‘yan takarar jam’iyyar na zaben 2027 tun a kwanaki.

APC Nigeria
Wani gangamin APC lokacin yakin neman zabe a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jam'iyyar APC ta fara tura sunayen 'yan takara

Labarin da aka samu daga jaridar The Nation ya ce Majalisar gudanarwa ta kasa ce ta ke da alhakin daura sunayen da ake yi a shafin hukumar zabe.

Kara karanta wannan

Magana ta canza da aka nemi sunayen wasu ‘yan takaran jam'iyyar APC aka rasa

Wasu a cikin masu neman takara sun tabbatar da cewa sun karbi fam da ake kira EC9 daga INEC a daren jiya, hakan ya tabbatar da sun samu tikiti.

Yanzu haka jam’iyya mai mulki ta tura wa INEC sunayen ‘yan takararta na majalisa a jihohin Ondo, Benuwai, Kwara da Kogi inda ake rikici kan tuta.

Zanga-zanga ta barke saboda batun takara

Irinsu Donald Ojogo da Festus Adefiranye sun samu takarar tazarce a APC. Daily Trust ta ce mata sun yi zanga-zangar cewa an canza 'yan takara a Ondo.

A bangaren sanatoci, an aika da sunayen Sanata Sunday Karimi, Sanata Prince Paul Ikonne, Sanata Emmanuel Udende da Sanata Adeniyi Adegbonmire.

Haka zalika akwai Sanata Titus Tartenger da Sanata Olajide Ipinsagba daga Benuwai da Ondo.

Wadanda suka yi zanga-zangar suna cewa an canza sunayen Hon. Gbenga Elegbeleye da Dr. Taiwo Fasoranti wadanda aka yi tunanin su za su yi takara.

Rahoton ya ce jam’iyyar ta tura sunayen Festus Olarewaju, John Odimayo, Abdulazeez Kaka da Samuel Okezie, Ekumankama Nkama da Abubakar Abdullahi.

Wasu ‘yan takaran da aka ce APC ta tura su ne Dr. Rafiu Ajakaye, Mohammed Mamman da Raheem Olawuyi. Za su fafata a zaben majalisar wakilai na kasa.

Kara karanta wannan

‘Dan majalisar APC da ya bi Obi da Kwankwaso zuwa NDC ya rasa kujerarsa

APC Nigeria
'Yan majalisar tarayya a bakin aiki a Abuja da hoton gangamin APC a 2023 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

APC ta fara raba fam din takara a Oyo

Masu takarar Majalisar tarayya da sanatoci a Oyo sun karbi fam a ranar Litinin daga hannun APC.

Idan rahoton da aka samu ya tabbata, Sharafadeen Ali da abokin gaminsa za su karbi nasu a ranar Alhamis, hakan zai kawo karshen burin Bayo Adelabu.

Duk wanda ya samu wannan fam zai cike shi da kyau kuma ya maida domin a mika wa INEC a karon karshe, daga nan sai a jira lokacin takara.

Za a cike fam din kuma a hada da takardun da ake bukata, sai a kai su bangaren fasahar zamani na ICT a jam’iyya, su kuma za su daura su a shafin INEC.

Wata majiya ta ce jam’iyyar APC ta wakilta ‘yan majalisar NWC su tsara yadda za a raba fam din a karkashin jagoranci shugabanni na kowace shiyya.

Rudanin 'dan takarar APC a Kaduna ta Arewa

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito da ake rade radin matsalar NDC ta jawo Kwankwaso zai koma PRP

Legit Hausa ta fahimci yadda magoya bayan Abdulazeez Kaka suka shiga farin ciki, suna cewa shi APC ta ba takarar Majalisar tarayya a Kaduna ta Arewa.

Su ma mutanen Hon. Samaila Sulaiman sun fito suna cewa gwaninsu ya cike fam kuma dama shi ne ya yi nasara a zaben tsaida gwani da aka yi a Mayu.

Adam Mohammed yana cikin mutanen Samaila Sulaiman a karamar hukumar Kaduna ta Arewa, ya yi magana da Legit Hausa.

Bayan karyata batun cewa an canza ‘dan takara, ya ce suna da kwarin guiwar yin nasara a kan Bello El-Rufai a babban zabe.

Malam Adam Mohammed ya ce ko a zaben 2023 da Bello El-Rufai ya yi nasara a kan Hon. Samaila Sulaiman, saboda mahaifinsa ne.

“Bello dan gwamna mai-ci ne lokacin, duka mutanen da ke gwamnatin mahaifinsa sun goyo masa baya domin faranta gwamna.
"Idan za a tuna, APC ta rasa duka kujerun Kaduna ta tsakiya tun daga sanatoci har majalisar dokokin jiha, amma ta ci Kaduna ta Arewa saboda yaron gwamna ne kuma karamar hukumarsa ne"

Yanzu mu ke da mulki, kuma shi Bello yana bangaren adawa, tunda muna da gwamnati, akwai aiki a gabansa

Kara karanta wannan

Takarar Gwamna: Yadda jam'iyyar ADC ta tsumbula cikin rikicin gida a jihar Katsina

Yaron Atiku ya yi kira ga jam'iyyun siyasa

Dazu aka rahoto cewa wani yaron Atiku Abubakar ya nemi ADC da PDP su yaki soke rajistar jam'iyyar NDC, yake cewa ‘dole mu dauki mataki’

Shehu Atiku Abubakar yana ganin idan aka tafi a haka, lamarin zai shafi sauran 'yan adawa, saboda haka ne ya kawo shawarar a fita zanga-zanga.

Ganin kotu ta soke rajistar NDC a ranar Juma'ar da ta wuce, an samu masu taya babbar jam’iyyar hamayyar takaicin mummunan abin da ya faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng