Dan Bilki Kwamanda: 'Dalilina na Ganawa da Atiku Abubakar'
- Korarren jigon APC, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda ya ce ziyartar Atiku Abubakar ba yana nufin ya fice daga APC ba mai mulkin Najeriya ba
- Ya bayyana haka duk da jam'iyyar ta sanar da korarsa saboda wasu dalilai, amma ya ce nace cewa har yanzu shi cikakken dan 'jam'iyya ne
- Dan Bilki Kwamnada ya ce tabbas ya yi kuskure a lokacin da ya tallafa APC a baya, kuma yanzu lokaci ya yi da za a gyara wannan kuskuren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Fitaccen jigo a siyasar Kano, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanada ya bayyana cewa akwai alaka mai kyau tsakaninsa da wasu manyan yan siyasar adawa duk da yana jam'iyyar APC.
Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Legit ta wayar tarho, inda ya ce yana da abokan siyasa da ya shafe shekaru 20 yana mu’amala da su.

Source: Facebook
A shafinsa na Facebook, Dan Bilki Kwamanda ya wallafa hotunansa da na dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar bayan sun kammala ganawa a Abuja.
Dan Bilki Kwamanda ya gana da Atiku
A tattaunawarsa da Legit, Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa zuwa wajen Atiku Abubakar girmamawa ce da kuma gaisuwa saboda jajircewarsa a siyasa.
Ya ce:
"Duk dan siyasa, wajibi ne ya girmama shi. Kuma za ki ga yanzu a Arewacin Najeriya ba mu da zakakurin dan siyasa irin mai girma Wazirin Adamawa."
"Don haka na kai masa wannan ziyara, amma mutane su daina daukar cewa wai saboda mutum yana wata jam’iyya, ba zai yi mu’amala da wasu mutane da ke wata jam’iyya ba."
Dan Bilki Kwamanda zai tallata takarar Atiku
A ganawar da muka yi da shi, Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa Nyesom Wike dan PDP ne, amma duk da haka ya zabi ya kashe jam’iyyarsa wajen raya APC.

Source: Facebook
Ya ce:
"Ni kin ga siyasa ta, ba haka take ba. A halin da Arewa take ciki, da halin bala’in rashin zaman lafiya da ake ciki, ga yunwa, ga tsadar rayuwa, ga talakawa sun shiga cikin halin kaka-naka-yi, ga ’ya’yanmu an mayar da su ’yan daba, ’yan shaye-shaye."
"Dole ne mu canza wa gyambo kaya, mu ga cewa waye zai kawo mana waraka daga wannan ta’addanci da sauransu, dole ne mu yi kowane, ba ma Atiku ba."
Ya kara da cewa sun yi kuskure, inda ya bayyana nadamarsa kan marawa APC baya har ta samu mulkin kasar nan, yana mai cewa a yanzu zai gyara wannan kuskure.
'Dan majalisa ya yi magana kan komawa APC
A wani labarin, kun ji cewa 'dan majalisar Kano Sulaiman Mukhari Ishaq Madobi ya ce komawarsu APC ya samo asali ne daga muradin yin abin da ya dace daa jama’a domin ci gabansu.

Kara karanta wannan
2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba
Ya shaidawa Legit yadda aka juyar da ra'ayin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi yunkurin komawa APC kafin a raba shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf daga baya saboda zargin son rai.
Hon Mukhari ya ce lokaci ya wuce da ake zabar mutum kawai saboda Jagora, yana mai cewa aikin da aka yi wa jama’a shi ne ya kamata ya zama abin dubawa saboda haka ya dace a sake zaben Abba.
Asali: Legit.ng

