Magana Ta Canza da Aka Nemi Sunayen Wasu ‘Yan Takaran Jam'iyyar APC Aka Rasa
- Jam’iyyar APC ta yi canje-canje ga jerin wadanda za su yi mata takara a zaben Majalisar dattawa da Majalisar wakilai a badi
- Sauyin zai iya jawo baraka sosai tsakanin ‘yan siyasar da aka cire sunansu bayan ayyana nasararsu da wadanda aka zakulo yanzu
- Wannan mataki da uwar jam’iyya ta dauka shi ne na karshe, ana sa ran wanda ya ga sunan shi ne zai yi wa APC takara a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Masu neman takara a mukamai dabam-dabam da suka rasa tikiti a APC sun yi kira ga jam’iyyar da ta bi a hankali wajen shirinta na zabe.
Wadanda suka sha kashi wajen samun tutar jam’iyyar APC sun yi gargadi cewa idan aka yi sake za a samu baraka saboda canza sunan ‘yan takara.

Source: Facebook
Rahoto daga Daily Trust ya yi karin haske game da yadda aka samu matsalolin tsaida ‘yan takara a jihohin Kaduna, Kwara, Ondo, Benuwai da Kogi.
Ba a san 'yan takaran majalisa a Kwara ba
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a reshen Kwara sun fara neman Mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki domin a zauna lafiya.
Yayin da aka ba ‘dan takarar gwamna fam, har yanzu an rasa su wane ne za su yi wa APC mai mulki takarar kujerun Majalisar Dattawa a Kwara a 2027.
Da farko an ce Lola Ashiru, Saliu Mustapha, da Umar Sadiq za su yi takara, amma yanzu an ji cewa APC ta canza sunayen ‘yan takarar sanata daga Kwara.
Labarin da ake samu shi ne an sauya su da sunayen AbdulRahman AbdulRazaq, Prince Olalekan Adewoye da Dr Mohammed Umar Mahamud.
Mutanen Akume sun yi galaba kan yaran gwamna
A Benuwai kuwa, ana cewa mutanen Sanata George Akume ne suke samun yadda suke so, jam’iyya ta ba su tikitin takarar Majalisar tarayya.
Da farko an ce Gabriel Suswam da Benjamin Aber sun samu takarar sanata a Benuwai, amma yanzu ana jin labari cewa jam’iyya ta canza su.
Business Day ta ce Titus Zam da Emmanuel Udende sun samu tikitin tazarce, kuma an canza wasu ‘yan takara na kujerun Majalisar wakilai a APC.
Jam'iyyar APC ta fuskanci zanga-zanga a Ondo
Sakamakon irin wannan canje-canje da aka samu a jihar Ondo, an ji cewa har ta kai wasu sun shirya zanga-zanga ganin an cire sunayen mutanensu.
APC ta canza ‘yan takaran sanatoci biyu cikin uku, sannan aka sauya duka mutane shida wadanda da farko aka ce za su yi takarar majalisar wakilai a 2027.

Source: Facebook
'Yan takara 2 a tikitin APC a Kaduna`
Rudanin da aka samu a Kaduna tsakanin Abdulazeez Kaka ne da Samaila Sulaiman, kowane bangare ya fito yana ikirarin shi ne ya samu takara.
Tsohon ‘dan majalisar Kaduna ta Arewa, Samaila Sulaiman shi ya doke Abdulaziz Kaka a zaben tsaida gwani, amma ana tunanin an nemi a canza shi.
Akwai wannan rigimar tsakanin Yusuf Zailani da Shehu Sani a takarar Sanatan tsakiyar Kaduna. Tsohon shugaban majalisar bai cire rai da samu tikiti ba.
Legit Hausa ta yi magana da Adam Mohammed, wani matashi da yake cikin manyan magoya bayan Hon. Samaila Sulaiman a Kaduna ta Arewa.
Malam Adam Mohammed ya tabbatar mana da cewa rade-radin da ake ji ba gaskiya ba ne, furofaganda ce kurum da ta fito daga ‘yan adawarsu.
"Ba komai ba ne illa furofaganda daga dayan bangaren domin kawar kawar mana da hankali wanda muna zargin akwai burbushin ‘yan adawa suna mara masu baya.
Matashin ya zargi wasu manya daga uwa duniya da daukar nauyin takarar abokin hamayyarsu, ya ce ba za a juya siyasar Kaduna daga jihar Legas ba.
“Kamar yadda ka sani ba a Twitter ake siyasa ba, daga gida ake yi kuma mun yarda da mutanenmu.”
- Adam Mohammed
Ana yi wa APC zanga-zanga a wasu jihohi
Dama can ana da rahoton zanga-zanga ta biyo bayan rabon fam, ana tsoron an canza wasu ‘yan takaran APC alhali suna jiran a fara yakin zabe.
Akwai yiwuwar a ga sauyi tsakanin wadanda suka lashe zaben tsaida gwani da wadanda APC za ta tsaida takara a karshe a wasu jihohin Najeriya.
Hakan ya biyo bayan uwar jam'iyya ta karbi korafi da aka samu bayan zaben fitar da gwani ko kuma tsarin maslaha da aka yi wajen tsaida 'yan takara.
Asali: Legit.ng


