Ministan Tinubu Ya Tayar da Rigima kan Hana Shi Takarar Gwamna, Ya Soki APC
- Tsohon ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu ya yi martani bayan rahoton cewa APC ta tsayar da dan takara a Oyo
- Adelabu ya ƙaryata rahoton cewa an tsayar da Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamna a Oyo domin zaɓen 2027
- Tsohon ministan ya bayyana cewa Bola Tinubu ya ba shi izinin barin mukaminsa domin fara shirye-shiryen neman kujerar gwamnan Oyo
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya yi watsi da matakin API kan dan takarar gwamna a Oyo.
Adelabu ya karyata cewa jam'iyyar da shugabannin APC amince da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamnan Oyo na bai ɗaya.

Source: Facebook
A ranar Juma’a ne wasu jiga-jigan APC a Oyo suka bayyana goyon bayansu ga Alli yayin wani taro da aka gudanar a Ibadan domin shirya zaɓen 2027, cewar TheCable.
Adelabu ya yi murabus saboda takara
Tsohon minista, Adebayo Adelabu ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin makamashi domin neman takarar gwamna a jihar Oyo.
Adelabu ya mika takardar ajiye aikinsa a hukumance ga sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, yau Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026.
Ya ba da shawarar kirkiro mukamin Ministan Makamashi mai kula da dukkan fannoni domin hada kai wajen gyaran bangaren wuta, gas da sauran fannoni.

Source: Facebook
Takarar Gwamna: Adelabu ya soki APC
Tsohon sanata Ayo Adeseun ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nuna goyon baya ga takarar Sharafadeen Alli, yana mai cewa ra’ayin shugaban ya kamata ya samu kulawa.
Sai dai Adelabu ya bayyana cewa kafin ya yi murabus daga matsayin ministan lantarki, ya nemi ganawa kai tsaye da Tinubu domin tattauna burinsa na takarar gwamna.
Yayin wani taron APC a Ibadan da Kudu maso Gabas, Adelabu ya ce shugaban ƙasa ya ba shi damar sauka daga mukami domin fara shirye-shiryen siyasa a Oyo.
'Yadda Tinubu ke goyon bayan Adelabu'
Adelabu ya bayyana cewa Tinubu ya shaida masa cewa ya daɗe yana son zama gwamna, kuma ba zai hana shi cika wannan buri ba, cewar Daily Post.
Ya ce shugaban ƙasar ya kuma bayyana yiwuwar cimma matsaya ta bai ɗaya tsakanin masu neman takara ko kuma gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye.
Tsohon ministan ya ce duk wanda ke cewa shugaban ƙasa ya amince da wani ɗan takara daban yana ƙarya domin shugaban bai sanar da hakan ga kowa ba.
Adelabu ya ƙara da cewa idan har Tinubu zai goyi bayan wani ɗan takara a Oyo, to shi ne zai fi dacewa da wannan goyon baya.
Adelabu ya fadi dalilin murabus daga minista
Mun ba ku labarin cewa tsohon ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya musanta rahotanni da ake yadawa cewa ya yi murabus ba tare da izinin Bola Tinubu ba.
Daya daga cikin hadimansa, Femi Awogboro ya ce sai da Shugaba Bola Tinubu ya amince kuma ya sa albarka kafin Adelabu da ajiye aiki.
Ya jaddada cewa tsohon ministan zai maida hankali wajen neman takarar gwamnan Oyo a zaben 2027, domin ci gaba da hidimata wa al'umma.
Asali: Legit.ng

