Shi ne Mafi Munin Shugaban Kasa a Tarihi In ji Tsohon Hadimin Tinubu

Shi ne Mafi Munin Shugaban Kasa a Tarihi In ji Tsohon Hadimin Tinubu

  • Tun da aka kafa Najeriya, Hakeem Baba-Ahmed yana da ra’ayin Bola Ahmad Tinubu shi ne mafi munin shugaba
  • A lokacin da kamfe ya gabato, Shugaban Najeriya ya kuma shan suka daga tsohon hadiminsa a Aso Rock
  • Hakeem Baba-Ahmed wanda yana cikin manyan Arewa ya koka cewa za a shiga uku idan Tinubu ya zarce a ofis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya saki sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a Najeriya.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed yana ganin tun da aka yi Najeriya, ba a taba samun shugabanci mafi muni irin na Bola Tinubu a yau ba.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana sa hannu a gaban manyan jami'an gwamnati a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Da aka yi hira da shi a tashar Symfoni TV, dattijon ya ce yankin Arewa ya mutu muddin shugaba Tinubu ya lashe zabe mai zuwa.

Ziyarar limaman katolika wajen Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Shugaban na PRP ya kuma caccaki Mai girma shugaban kasa saboda yadda ya saba wa matsayar limaman katalolika da suka ziyarce shi.

A lokacin da shugabannin darikar katolika suka zauna da Tinubu a Aso Rock, sun nuna masa cewa abubuwa ba su tafiya daidai a kasa.

Fadar shugaban kasa ta yi wuf ta yi watsi da korafin malaman addinin, Hakeem Baba-Ahmed ya ce hakan ya nuna raunin shugaba Tinubu.

Tsohon shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattawan yana ganin akwai matsala a yadda ziyarar jagororin kiristocin ya kasance kwanaki.

Hakeem Baba-Ahmed ya ce:

"Duk batun da limaman suka kawo, shugaban kasar ya ce a’a, ba haka ba ne. Ni ne nake kan daidai.
"Babu yunwa a kasar nan, abin da ku ke fada ba gaskiya. Haba don Allah, shugaban kasar da ya san abin da yake yi, wanda yake rike da kasa ba zai yi wannan ba."

Makomar Arewa idan Tinubu ya koma mulki

Jagoran adawar ya kuma caccaki Tinubu saboda abin da ya kira rashin sanin halin da mutane suke ciki, Daily Post ta zo da wannan labari.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya juyawa Atiku baya, ya ce ba ya son ɗan Arewa ya zama shugaban ƙasa a 2027

"Arewa za ta mutu idan Tinubu ya ci zabe a 2027. Shi ne mafi munun shugaban kasa a tarihin Najeriya.
"Matsalar ita ce akwai yankewar alaka tsakanin gwamnati da mutanenta."

- In ji Hakeem Baba-Ahmed

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da mai dakinsa Remi Tinubu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban na PRP ya zargi gwamnati mai-ci da daukar hakkokin Arewa tana mika wa yankin Kudu saboda 'yan siyasarsu sun bi bayan shi.

A hirar, Hakeem ya soki gwamnonin Arewa 18 da suka bi bayan Tinubu, ba su iya fada masa gaskiya, yana cewa hakan yana da hadari ga yankin.

Bayani game da yunkurin juyin mulki

Wani rahoto ya kawo abubuwan da aka tattaro daga yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu da wasu jami'an sojoji suka yi a shekarar 2025.

An samu bayanai game da shiri da lokacin hambarar da mulkin farar hula har zuwa rabon mukamai da sojoji sun iya kifar da gwamnatin Najeriya.

Bayanai sun nuna yadda Kanal Mohammed Ma'aji ya so yin amfani da kan bindiga wajen ganin ya kawo karshen mulkin farar hula a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng