"Kiristoci na Cikin Matsala"; Malamin Addini Ya Dauki Zafi kan Kalaman Sheikh Jingir
- Primate Elijah Ayodele ya soki gwamnatin tarayya kan zargin yin shiru game da kalaman da ake dangantawa da Sheikh Sani Yahaya Jingir
- Ayodele ya ce ya kamata a kama Sheikh Jingir saboda kalaman da ya yi, yana gargadin cewa hakan na iya barazana ga zaman lafiya
- Shugaban cocin ya bukaci gwamnatin Tinubu ta gargadi shugabannin addini kan kalaman da ka iya haddasa rikicin addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya soki gwamnatin tarayya kan zargin yin shiru game da wasu kalaman da ake dangantawa da malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Ayodele ya ce ya kamata a kama Jingir kan kalaman, yana gargadin cewa rashin daukar mataki kan shugabannin addini da ke yin kalaman tayar da hankali na iya yin barazana ga zaman lafiya da zaman tare a Najeriya.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, yayin da yake martani kan wata magana da aka danganta wa Jingir, cewar rahoton jaridar Vanguard.
An dai ruwaito cewa malamin ya ce wadanda ba su amince da tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi ba su bar Najeriya.
Hakazalika, an kuma ruwaito cewa Jingir ya bayyana Kiristoci a matsayin “kafirai” a cikin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Malamin addinin musuluncin ya kuma bukaci jama'a da su gyara kuri'unsu domin nunawa duniya cewa Musulmai suna da yawan da babu wanda ya kai su a Najeriya.
Primate Ayodele ya yi martani kan kalaman Jingir
Primate Ayodele ya mayar da martani ne a wani bidiyo da Tunde Ednut ya wallafa, inda ya yi zargin cewa da wani shugaban addinin Kirista ne ya yi irin wannan magana, da gwamnati ta dauki mataki daban.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Sheikh Jingir ya yi ƙarin bayani kan kalamansa da suka tayar da ƙura a Najeriya
“Idan gwamnati ba ta yi gargadi kan wannan ba, to Kiristanci na cikin matsala a Najeriya. Wannan tsohon wawa marar hankali, malamin addinin Musulunci Jingir, ya kamata ya kasance a gidan yari a yanzu.” In ji shi
Primatea Ayodele ya kara da cewa:
“Da Kirista ne ya yi irin wannan magana, da nan take sun kama shi.”
An bukaci a ja kunnen Sheikh Jingir
Malamin addinin ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta gargadi Jingir da sauran shugabannin addini kan yin kalaman da ka iya kara rura wutar rikicin addini.
Ayodele ya kuma yi gargadin cewa rashin daukar mataki kan kalaman da ke tayar da hankali na iya kara raunana zaman lafiya da hadin kan kasa.

Source: Facebook
Sheikh Sani Yahaya Jingir bai yi nadama ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin musulunci kuma shugaban kungiyar Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya kare matsayarsa kan tallata muslim-muslim.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa ba ya nadamar goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya domin yana da 'yancin yin hakan.
Malamin addinin musuluncin, Sheikh Jingir ya bayyana cea baya nadamar ne duk kuwa da irin sukar da kalamansa wajen tallata muslim-muslim suka jawo.
Asali: Legit.ng
