Masarautar Kano Ta Tsoma Baki a kan Shirin Zaben 2027, Ta Tura Sako ga Ƴan Najeriya

Masarautar Kano Ta Tsoma Baki a kan Shirin Zaben 2027, Ta Tura Sako ga Ƴan Najeriya

  • Masarautar Kano da malaman addinin Musulunci sun hango abin da ya dace yan Najeriya su yi gabanin babban zaben 2027 mai zuwa da tsaro
  • Shugabannin addini sun ce tarbiyyar yara bisa koyarwar Alƙur’ani na da muhimmiyar rawa wajen samar da al’umma mai zaman lafiya da ɗorewar tsaro
  • Sun kuma yi kira ga waɗanda suka kammala karatun Alƙur’ani da su zama jakadu na zaman lafiya, haƙuri da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Masarautar Kano da malaman addinin Musulunci sun yi kira ga ’yan Najeriya da su yawaita addu’o’in samun zaɓen 2027 cikin zaman lafiya, gaskiya da nasara.

Sun kuma, tare da yi gargaɗin cewa zaman lafiyar ƙasar zai dogara ne matuka kan yadda ’yan ƙasa da shugabanninsu za su rungumi haƙuri, da’a da kuma ɗabi’ar da ta dace.

Kara karanta wannan

An kashe mutane 18 ana saura kwana 6 zaben gwamna, APC ta rasa mambobi 10

Masarautar Kano ta yi magana game da yi wa kasa addua
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a Fada Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Twitter

Arise News ta kawo labarin cewa an yi wannan kiran ne a wani taron yaye ɗaliban da suka kammala karatun Alƙur’ani mai girma, inda shugabannin gargajiya da na addini suka yi amfani da wajen wajen kira da a ƙara ƙarfafa tarbiyyar yaran Najeriya.

Kiran masarautar Kano ya yan Najeriya

Jairdar The Nation ta wallafa cewa da yake wakiltar Sarkin Kano a wajen taron, Sadaukin Kano, Awal Ado Bayero, ya taya ɗaliban da suka kammala karatun da iyayensu murna.

Sai dai ya buƙaci ɗaliban da su fahimci cewa kammala karatun Alƙur’ani ba ƙarshen tafiya ba ne, illa dai farkon hanyar da za ta buƙaci su yi aiki da darussan da suka koya.

Malamai da masarautar Kano sun nanata muhimmancin yi wa kasa addu'a
Wani 'dan Najerya ya na kada kuri'arsa a yayin zabe Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Bayero ya ce koyarwar Alƙur’ani na da muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya, kyakkyawar mu’amala da ɗabi’a, da kuma samar da ’yan ƙasa masu ɗaukar nauyin al’amuransu, musamman a lokacin da Najeriya ke shirin gudanar da zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Abin ɓoye ya fito fili, an gano dalilin Tinubu na ƙara rundunar sojoji

Ya ce:

“Yayin da muke tunkarar babban zaɓen 2027, muna addu’ar yaran nan su ci gaba da yi wa ƙasa addu’a, sannan Najeriya ta samu sahihin zaɓe da zaman lafiya."

Bukatar masarautan Kano ga daliban Kur'ani

Ya kuma buƙaci waɗanda suka kammala karatun da su ci gaba da karatun Alƙur’ani da haddace shi, tare da kira ga iyaye da manya da su tabbatar da cewa an gadar da darussan da ke cikin Littafi Mai Tsarki ga ’ya’yansu da jikokinsu.

A cewarsa, ilimin addini da tarbiyya na da matuƙar muhimmanci wajen gina matasa masu amfani ga al’umma da kuma kare kansu daga mummunan tasiri.

Sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron suka danganta tarbiyyar yara da babban ƙalubalen samar da Najeriya mai zaman lafiya da tsaro.

Gwamnan Kano ya yi gaba

A baya, mun kawo labarin cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake samun lambar yabo kan kokarin da yake yi na kafa shigabanci nagari Ƙungiyar NAWOJ ta karrama.

Kara karanta wannan

An ji dalilin Saudiyya da ta garkame wasu 'yan Najeriya a gidan yari

Gwamna Abba Kabir Yusuf da lambar yabo kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari wanda kungiyar yan jaridu mata ke ganin ya yi zarra a bagaren tabbatar da an samu kwanciyar hankali a Kano.

An gabatar da lambar yabon ne a taron mata yan jarida kan tsaro na Women In Security Summit and Awards 2026 wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja domin kara karfafa gwiwa wajen samar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng