‘Dan Majalisar APC da Ya Bi Obi da Kwankwaso zuwa NDC Ya Rasa Kujerarsa

‘Dan Majalisar APC da Ya Bi Obi da Kwankwaso zuwa NDC Ya Rasa Kujerarsa

  • Hon. Collins Egbetamah ya sanar da Majalisar Delta cewa ya yi murabus daga jam’iyyar APC mai rinjaye da mulki a jihar
  • Ganin a jam’iyyar APC aka zabe shi kuma ya samu kujerar da yake kai, matakin ya jawo ya rabu da matsayin da yake kai
  • A matsayin Shugaban majalisar dokoki¸ Rt. Hon. Dennis Guwor ya yi umarni INEC ta yi haramar shirya zaben cike gurbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Delta - Majalisar dokokin jihar Delta ta ayyana wata kujera cewa babu mai ita a sakamakon sauya-sheka da wanda yake kai ya yi.

An saba jin an yi wa masu mukamai musamman na majalisa barazanar rasa kujerunsu idan suka rabu da jam’iyyar da ta ba su nasara.

Hon. Collins Egbetamah Hoto: Egbetamah Ovie Collins
‘Dan Majalisar Udu a jihar Edo lokacin yana ofis Hoto: Egbetamah Ovie Collins
Source: Facebook

Collins Egbetamah ya rasa kujera a Majalisar Delta

Hon. Collins Egbetamah ya samu kan shi a matsala kuma yana iya rasa kujerar da yake kai a cewar wani rahoto da Leadership ta fitar.

Kara karanta wannan

Soke rajista: Daga jin hukuncin kotu, na hannun daman jagoran NDC ya ruga APC

A dalilin sauya shekar da Hon. Collins Egbetamah ya yi daga jam’iyyar APC zuwa NDC, Majalisar jihar Delta ta ce ya rasa kujerarsa.

Majalisar dokokin ta kuma bukaci akawunta da ya sanar da hukumar INEC cewa babu wanda yake kan wannan kujera a yanzu.

Ana so INEC ta yi zaben cike gurbin majalisa

An bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta shirya sabon zaben cike gurbi domin a samu wanda zai canje shi a Majalisar Delta.

Wannan mataki ya zo ne bayan duka ‘yan majalisar sun yi na’am da zancen da Emeka Nwaobi, ya bijro da shi a wani zama da aka yi.

Nwaobi shi ne Shugaban masu rinjaye kuma rokon na shi ya samu goyon bayan mataimakin shugaban majalisa, Hon. Arthur Akpowowo.

Premium Times ta ce Rt. Hon. Dennis Guwor ya jagoranci zaman majalisar da aka dauki wannan mataki a ranar 30 ga watan Yuni 2026.

Kundin tsarin mulki ya yi maganar sauya-sheka

Dennis Guwor ya kafa hujja da sashe na 109(1)(g) & (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

APC ta taɓa sunaye kafin mika wa INEC jerin ‘yan takara a zaben 2027

Shugaban majalisar ya ce abin da doka ta tanada shi ne ‘dan majalisa zai rasa kujerarsa idan ya canza sheka kafin karshen wa’adinsa.

Kundin tsarin mulkin Najeriya bai halatta a rabu da jam’iyyar da ta kawo mutum kan kujera ba sai ta halin da doka ta san da zaman shi.

Hon. Collins Egbetamah
Peter Obi yana tafiya tare da masoya da Hon. Collins Egbetamah a Majalisar Delta Hoto: Egbetamah Ovie Collins/Esther Umoh
Source: Facebook

Gabanin nan, Egbetamahy a gabatar wa ‘yan majalisa da wasika mai dauke da kwanan watan 19 ga Yuni cewa ya yi murabus daga APC.

Tun a ranar 30 ga watan Yuni 2026 ya yi sallama da APC domin ya cin ma burinsa na siyasa, yana kuma mai godewa ‘yan tsohuwar jam’iyyarsa.

Rahoton ya ce wannan ‘dan siyasa da ya yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki ya kasance yana wakiltar mazabar Udu a majalisar jihar Delta.

Yaron Atiku ya tsaya wa jam'iyyar NDC

A labaran da aka kawo a baya, an ji wani yaron Atiku Abubakar ya nemi ADC da PDP su yaki soke rajistar NDC, yake cewa ‘dole mu dauki mataki’.

Shehu Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da soke rajistar jam'iyyar kuma ya yi kira ga jam'iyyun PDP, ADC, da sauran ƙungiyoyi su haɗa kai su yi zanga-zanga.

A cewarsa, dole ne 'yan adawa su tashi tsaye domin kare tsarin dimokuradiyya ko kuwa a koka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng