Bayanai Sun Fito da Ake Rade radin Matsalar NDC Ta Jawo Kwankwaso Zai Koma PRP
- Akwai jita-jita cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya raba kafa ta hanyar fansar fam din neman takara a jam’iyyar PRP
- Ganin yanzu jam’iyyar NDC tana fuskantar barazanar gagara shiga takara, an dawo yada wannan labari da bai da tushe
- Theo Abu Agbada ya fito ya karyata rade-radin, ya kuma tabbatar wa duniya cewa manyan NDC ba za su canza sheka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Tun tuni aka yi ta yawo da wani labari da ba a tabbatar ba cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya saye fam a boye a jam’iyyar PRP.
Ana zargin ‘dan siyasar ya fanshi fam din takara a asirce ne domin shi da mutanensa su tsallaka PRP idan aka samu wata matsala a NDC.

Source: Facebook
Jita-jitar barin Rabiu Kwankwaso NDC
A shafin X, Theo Abu Agada ya karyata jita-jitar da ake ji cewa wani daga cikin masu takarar shugaban kasa a NDC yana shirin canza gida.

Kara karanta wannan
Takarar Gwamna: Yadda jam'iyyar ADC ta tsumbula cikin rikicin gida a jihar Katsina
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad yana cikin wadanda suka rika yawo da wannan jita-jita a dandalin X a karshen makon jiya.
Ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni 2026, Bashir Ahmad ya yi magana game da hukuncin kotun da ya soke rajistar da aka yi wa jam’iyyar NDC.
“Ina jin rahoto cewa daya daga cikin masu takara a zaben shugaban kasa a NDC yana tunanin koma wa PRP sakamakon ukuncin da ya cire jam’iyyar (NDC) daga cikin jam’iyyun siyasar da doka ta san da zamansu.
Za mu jira, mu ga yadda abubuwa za su kasance.”
Bashir Ahmaad ya yi wannan magana kenan sai Mista Theo Abu Agada ya maida masa martani a jiya.

Source: Twitter
Darektan yada labaran NDC ya amsa Bashir Ahmad
"Wannan karya ce ‘danuwa na. Shugabanninmu suna ta yin zama kuma da gaske suke yi a lamarin NDC.
Kowane daga cikinsu a jam’iyyar NDC ya dage wajen ganin cewa tsarin damukaradiyya na jam’iyyu dabam-dabam ya wanzu a Najeriya."
- Theo Abu Agbada
Duk da amsar da ya bada, matashin ‘dan siyasar bai tsaya nan ba, ya tuna masa yadda aka yi irin wadannan maganganu kafin wasunsu su bar ADC.
A tsakiyar shekarar nan ne Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka shiga NDC daga jam’iyyar ADC.
Malam Bashir Ahmad ya fada wa Theo Agbada cewa idan shugabannin na NDC ba su samu abin da suke so ba, babu mamaki su sake sauya sheka.
Sodiq Tode, wani masoyin Atiku Abubakar shi ma ya maida masa amsa a X, yake cewa a zura masu ido da kyau, za su iya koma wa wata jam’iyya.
Ana ganin Peter Obi zai iya barin NDC
“Ku sa masu ido da yau. Don suna halartar taron masu ruwa da tsaki a NDC bai hana Obi/Kwankwaso koma wa wata jam’iyyar.
Sun halarci duka taron ADC, sun je zaman da aka yi a Ibadan kuma su ka bar jam’iyyar bayan ‘yan kwanaki. Obi ya sha alwashi sai ya yi takara.
- Sodiq Tode
Wani mai suna @Tony_Ogbuagu ya yi makamancin wannan magana, yana tuna yadda Peter Obi ya rabu da jam’iyyar ADC bayan an faro tafiya da shi.
NDC: Hankalin Obi da Kwankwaso ya tashi
Kun ji labarin yadda abin da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka guje wa a ADC ya biyo su jam'iyyar har NDC, yanzu za a garzaya kotun daukaka kara a Najeriya.
Hukuncin alkalin kotun tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ya tada hankalin shugabanni da ‘ya ‘yan jam’iyyar NDC da soke mata rajista da aka yi a karshen makon jiya.
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da za su yi takara a jam’iyyar hammayar sun shiga yin zama na gaggawa dabam-dabam a Abuja da nufin su daukaka kara a kotu.
Asali: Legit.ng

