Gwamnatin Kebbi Ta Fadi Watannin da za Ta Tsaya da Kafarta ba Tallafin Tarayya

Gwamnatin Kebbi Ta Fadi Watannin da za Ta Tsaya da Kafarta ba Tallafin Tarayya

  • Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya ce gwamnatinsa na da isasshen tsari na kula da kudade da zai ba ta damar biyan albashi da fansho na tsawon watanni
  • Kwamred Nasir Idris ya bayyana cewa jiharsa za ta iya daukar nauyin ma'aikatan ba tare da an jira kudin da ke shigowa duk wata daga tarayya ba
  • Ya ce tun bayan hawansa mulki ya dauki ma’aikata 5,166, ciki har da likitoci, ma’aikatan lafiya da ma’aikatan jinya domin kara bunkasa harkar lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi - Gwamnan ya tabbatar da cewa Kebbi za ta kasance cikin jihohin farko da za su fara biyan sabon mafi karancin albashi idan an kammala tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.

Kara karanta wannan

Bayan rahoton Legit Hausa, gwamna ya gana da matashin da ya daina tallata Tinubu

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ce ya samar da tsarin kula da kudaden gwamnati cikin tsanaki da bin ka’ida, wanda zai ba gwamnatinsa damar biyan albashi da fansho na tsawon watanni biyar a jere.

Nasir Idris ta yi wa yan kwadago alkawari
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Sarki Yahaya
Source: Facebook

Channels TV ta ce ya Gwamnan ya ce za a iya biyan kudin ne ba tare da samun komai daga Asusun Tarayya na FAAC ba saboda tsarin da ake da shi.

Kebbi za ta biya albashi - Gwamna

A ruwayar jaridar Leadership, Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 12 ga watan Agusta, 2026 a Birnin Kebbi, yayin bude taron ma’aikatan lafiya da Majalisar Ma’aikatan Lafiya ta Jihar Kebbi ta shirya.

Majalisar ta kunshi Kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya, kungiyar masana kimiyyar dakunan gwaje-gwaje ta Najeriya, kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, ma’aikatan dakin gwaje-gwaje da kuma ta masana magunguna ta Najeriya.

Nasir Idris, wanda tsohon shugaban kasa na Kungiyar Malaman Najeriya ne kuma tsohon mataimakin shugaban NLC, ya ce har yanzu yana daukar kansa a matsayin jagoran kwadago.

Nasir Idris ya ce gwamnatinsa za ta iya tsayawa da kafarta
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Ba zan bar ku ji kunya ko na bata muku rai ba, har yanzu ina daya daga cikinku. Lokacin da na hau mulki a matsayin gwamna, na cire dokar hana daukar ma’aikata, sannan na dauki sabbin ma’aikata 5,166 a ma’aikatan gwamnati, ciki har da likitoci, ma’aikatan lafiya da ma’aikatan jinya.”

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

An samu ci gaba a Kebbi

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar Kebbi ta samu gagarumin ci gaba a bangaren kiwon lafiya, tare da aiwatar da sabon tsarin albashin ma’aikatan lafiya da likitoci.

Ya kara da cewa:

“Ko da akwai kudade daga FAAC ko babu, zan iya biyan albashi da fansho na tsawon watanni biyar a jere, saboda gwamnatina ta yi amfani da tsarin kula da kudade cikin tsanaki da bin ka’ida.”

Dangane da sabon mafi karancin albashi, Idris ya ce Kebbi za ta kasance cikin jihohin farko da za su fara aiwatar da sabon tsarin biyan albashin bayan kammala tattaunawar da ke tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya.

Alkawarin gwamnan Kebbi

A baya, kun samu labarin cewa gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya yi alkawarin tallafa wa iyalan ’yan sanda 10 da ’yan ta’adda suka kashe yayin gudanar da ayyukan tsaro.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da tawagar babban sufeton ’yan sanda, Olatunji Disu, ta kai masa ziyarar ta’aziyya a Birnin Kebbi bayan rasuwar jami'an tsaro a jihar.

Mataimakin babban sufeton ’yan sanda, Umar Dada, ya ce rundunar za ta ƙara ƙoƙari wajen kama waɗanda suka kai harin wanda ya jikkata jama'a da salwantar da rayukan jami'an.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng