Ministocin Tinubu: Sanata Karimi Ya Nemi Kawo Wa El-Rufai Cikas Yayin Tantance Shi a Majalisa

Ministocin Tinubu: Sanata Karimi Ya Nemi Kawo Wa El-Rufai Cikas Yayin Tantance Shi a Majalisa

  • An samu 'yar ƙaramar hayaniya a Majalisar Dattawan Najeriya yayin da ake ci gaba da tantance ministocin Tinubu
  • Sanata Sunday Karimi, da ke wakiltar Kogi ta Yamma ne ya janyo hayaniyar saboda tambayar da ya yi wa El-Rufai
  • Sanatan ya nemi a ba shi damar yi wa El-Rufai tambayoyi dangane da matsalolin tsaro da aka riƙa samu a Kudancin Kaduna lokacin da yake gwamna

Abuja - An ɗan sami wata 'yar ƙaramar dirama a zauren Majalisar Dattawan Najeriya, yayin da wani sanata ya nemi kawowa Nasir El-Rufai cikas a yayin da ake tantance shi.

Sanata Sunday Karimi, wanda ke wakiltar Kogi ta Yamma ne ya nemi kawo ruɗani a cikin tantancewar da ake yi wa El-Rufai kamar yadda The Punch ta wallafa.

An nemi a tayarwa da El-Rufai hankali
Sanatan Kogi ya nemi ya kawowa El-Rufai cikas a Majalisar Dattawa. Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Menene sanatan ya fadawa El-Rufai? Karin bayani

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Ƙasa Rasuwa a Nahiyar Afirka

Bayan El-Rufai ya kammala jawabinsa a gaban majalisar, Sanata Sunday Karimi ya miƙe inda ya bayyana cewa yana da ƙorafin da yake son gabatarwa a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karimi ya bayyana cewa ƙorafin da yake da shi a kan El-Rufai shi ne a kan matsalolin tsaro da aka riƙa samu a kudancin Kaduna lokacin da yake gwamnan jihar.

Bayan hakan ne Karimi ya miƙa takardun koken na sa ga mataimakin shugaban Majalisar Dattawan, Barau Jibril kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Daga nan ne Karimi ya nemi shugaban Majalisar Dattawan ya ba shi izini domin ya karanto ƙorafin na sa.

Sai dai shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bai saurari ƙorafin da Karimi ya zo da shi ba, inda ya ce ma sa ba yanzu ba ne lokacin tattauna korafe-korafe.

El-Rufai ya amsa tambayoyin da Abdulaziz Yari ya yi masa

Kara karanta wannan

El-Rufai: Tinubu Ya Shirya Magance Matsalar Wutar Lantarki a Cikin Shekara 7

Bayan gama zayyano aikace-aikacen da ya yi a lokacin da yake Gwamnan Kaduna da kuma lokacin da yake ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, El-Rufai ya amsa wasu tambayoyi da aka yi ma sa.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, kuma sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Arewa, Abdulaziz Yari Abubakar ne ya yi ma sa tambaya ta farko.

Bayan tambayar ta Yari, sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Arewa, Suleiman Kwari ya nemi majalisar ta bai wa El-Rufai izinin miƙa gaisuwar ban girma, sannan ta sallame shi.

Bayan amsa tambayar ta Yari ne shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya bai wa El-Rufai damar tafiya bayan kwasar gaisuwa.

Sunayen mutane 5 da ake hasashen Tinubu zai ba minista daga Kano

Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan mutane biyar da ake hasashen Shugaba Tinubu zai iya zaɓowa a matsayin ministoci daga Kano.

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa MS Ingawa ne ya wallafa sunayen a wani rubutu da ya ɗora a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Fadi Manyan Dalilai 13 Da Bai Kamata ‘Yan Najeriya Su Goyi Bayan Mamayar Jamhuriyar Nijar Ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel