An Bude Damar Shiga Shirin da Matasa Za Su Iya Samun Naira Miliyan 5 a Najeriya

An Bude Damar Shiga Shirin da Matasa Za Su Iya Samun Naira Miliyan 5 a Najeriya

  • Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria da abokan hulɗarsa sun ƙaddamar da gasar Nigeria PachiPanda Challenge ta 2026 ga matasan Najeriya
  • Wannan gasa wata dama ga matasa masu shekaru 18 zuwa 35 da ke da basirar ƙirƙire-ƙirƙire da harkokin kasuwanci
  • Za a raba kyautar Naifa miliyan 10 ga mutane uku da suka samu nasara, yayin da za a zaɓi ‘yan takara 10 domin shiga sansanin horaswa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An bude damar shiga gasar Nigeria PachiPanda Challenge ta 2026, wacce za ta bai wa matasa damar samun Naira miliyan 2 zuwa 5 a Najeriya.

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria tare da asusun WWF), ta hannun gidauniyar NCF, shirin majalisar dinkin duniya na UNDP da Deloitte Nigeria, ne suka ƙaddamar da gasar ta bana.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan Najeriya za su nemi tallafin ECOWAS na dala 65,000

PachiPanda Challenge
Wasu daga cikin matasa tare da shugabannin shirin PachiPanda Challenge Hoto: @arisetv
Source: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa gasar, wadda aka gudanar da ita karo na uku, an shirya ta ne domin tallafa wa matasa masu basira da ‘yan kasuwa wajen samar da hanyoyin magance matsalolin muhalli.

Abubuwan da gasar ta mayar da hankali

Taken gasar ta bana shi ne “Nature meets innovation: unlocking Africa’s green economy”, kuma tana buɗe ga matasa masu shekaru 18 zuwa 35, ‘yan kasuwa da masu kanana da matsakaitan masana’antu.

Masu shiga gasar za su ƙirƙiri hanyoyin magance matsalolin muhalli a Najeriya a fannoni huɗu da suka haɗa da sauyin yanayi, birane masu jure sauyin yanayi, kare muhalli a al’umma da kuma yaƙi da gurɓatar muhalli.

Masu neman shiga za su iya yin takara su kaɗai ko cikin ƙungiyar da ba ta wuce mutum uku ba.

Za a rabawa matasa Naira miliyan 10

Masu shirya gasar sun ce za a zaɓi ‘yan takara 10 daga cikin wadanda suka shiga domin horaswa na tsawon kwanaki huɗu da kuma taron gabatar da ayyuka a Legas.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yayyafa ruwan sanyi bayan kalaman Jingir sun ta da kura

Za a horas da ‘yan takarar kan dabarun kasuwanci, yadda ake gabatar da ra’ayoyi da kuma inganta ayyukansu domin su samu damar yin tasiri mai ɗorewa.

Daga bisani, kwamitin ƙwararru zai saurari gabatarwar ƙarshe, inda uku na farko za su raba kyautar N10m. Wanda ya zo na farko zai samu N5m, na biyu N3m, yayin da na uku zai samu N2m.

Wadanda suka yi nasara za su kuma samu damar yin hulɗa da ƙwararru da cibiyoyin tallafi domin bunƙasa ayyukansu. Za su wakilci Najeriya a gasar Africa PachiPanda Finale, kamar yadda tashar Arise TV ta rahoto.

MTN Nigeria.
Dan karamin shagon rijistar layukan MTN a Najeriya Hoto: MTN Nigeria
Source: UGC

MTN ya bayyana manufar gasar

Babban Jami’in Ayyukan Kamfani da Dorewar Muhalli na MTN Nigeria, Tobe Okigbo, ya ce shirin ya nuna muhimmancin haɗa kula da muhalli da ci gaban tattalin arziki.

Ya ce:

“A matsayinmu na kamfani da ke da alaƙa sosai da al’ummomin da muke yi wa hidima, mun fahimci cewa kula da muhalli da ci gaban tattalin arziki dole ne su kasance tare.”

An buɗe neman shiga gasar tun ranar 29 ga Yuli, kuma za a rufe karɓar bukatun shiga ranar 28 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Yadda barazanar Iran ta firgita Trump, ya sauya jirgi saboda tsoron kashe shi

ECOWAS ta bude shafin raba tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ECOWAS ta buɗe shafin neman tallafin kasuwanci a karo na biyu, inda za a raba kyaututtukan kuɗi da suka kai $65,000.

ECOWAS ta buɗe neman tallafin ranar 3 ga Agusta, 2026, kuma za a rufe shafin karɓar bayanai a ranar 31 ga Agusta, 2026

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262