An Zo Wajen: An Fara Shirin Hana Jam'iyyar Su Kwankwaso Shiga Zaben 2027

An Zo Wajen: An Fara Shirin Hana Jam'iyyar Su Kwankwaso Shiga Zaben 2027

  • Jam'iyyar adawa ta NDC da Rabi'u Kwankwaso da Peter Obi ke cikinta ta fara fuskantar sabuwar barazanar shari'a bayan maka ta a gaban kotu a Abuja
  • Hakan ya zo ne bayan jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa ba su da wata matsala a kotu yayin taron da suka yi a kwanakin baya
  • Wanda ya shigar da karan, Ahidjo Karlahi ya yi zargin cewa jam'iyyar ta saba dokokin Najeriya, inda ya bukaci kotu ta soke ta tare da haramta mata shiga harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mukaddashin shugaban tsare-tsare na kungiyar ADA, Ahidjo Karlahi, ya shigar da kara a kan jam’iyyar NDC yana neman hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta soke rajistarta.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da shari'ar da aka nemi soke rijistar ADC da wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya

An shigar da karar ne a makon da ya gabata ranar Talata a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kuma kotun ta mika karar ga mai shari’a Mohammed Umar.

Jagororin NDC a wajen taro
Sanata Rabiu Kwankwaso da wasu manyan NDC a Abuja. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa jagoran jam’iyyar NDC, Seriake Dickson, ya bayyana cewa babu kara da aka kalubalantar rajistar jam’iyyar.

Dickson, wanda ya yi magana a taron farko na kasa na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, ya dage cewa an yi wa jam’iyyar rajista bisa doka kuma tana hade gabanin babban zaben shekarar 2027.

Korafin da ake a kan NDC a kotu

A cikin takardar karar da Ahidjo Karlahi ya gabatar, ya ce NDC ba ta cika sharudan kundin tsarin mulki da dokokin zabe suka tanada ba.

Karlahi, wanda ya sanya INEC da NDC a matsayin wadanda ake kara na farko da na biyu, ya kafa hujjar cewa ba a sanya NDC cikin kungiyoyin da aka tantance domin neman rajista a aikin rajistar jam’iyyun siyasa na shekarar 2025 ba.

A cewarsa, NDC ta kauce wa dukkan matakan da suka zama wajibi a tsarin rajista, saboda haka bai kamata a yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa a kasar nan ba.

Kara karanta wannan

'Zaben Peter Obi da Kwankwaso kamar ba Tinubu damar nasara ne a 2027'

Trust Radio ya rahoto ya ce:

“Ba a sanya NDC cikin kungiyoyin da aka tantance domin neman rajista a aikin rajistar jam’iyyun siyasa na shekarar 2025 ba;
“Ba a sanya NDC cikin kungiyoyin da suka biya kudin gudanarwa N2,000,000.00 kuma suka samu shiga dandalin neman rajista na INEC ba;
“NDC ba ta shiga dandalin rajistar jam’iyyun siyasa na INEC a lokacin aikin rajistar shekarar 2025 ba, wanda shi ne kadai hanyar cike fom din EC15A;
“Saboda haka NDC ba ta cike fom din EC15A na INEC ba, wanda shi ne kadai ingantacciyar hanyar neman rajista a matsayin jam’iyyar siyasa; kuma
“Ba a sanya NDC cikin kungiyoyin siyasa da INEC ta wallafa a matsayin wadanda suka nemi rajista ba. Wadannan abubuwa ne da suke a fili a cikin bayanan hukuma.”
Manya 'yan NDC a Najeriya
Lokacin da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suka ziyarci jagoran NDC a Abuja. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Twitter

Abin da ake so kotu ta yi wa NDC

Jigon ADA din ya roki kotu ta bayyana rajistar da NDC ta ce ta yi a matsayin abu da ya saba wa kundin tsarin mulki, ba bisa ka’ida ba, haramtacce, ya wuce iko kuma marar inganci.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Hakeem Baba Ahmed ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi murabus

Ya kara da cewa:

“ina rokon kotu ta:
“Bayyana cewa kundin tsarin mulki bai amince a yi wa wata kungiya rajista ba tare da ta cika sharudan da kundin tsarin mulki ya tanada ba sannan ta ci gaba da cin gajiyar matsayin jam’iyyar siyasa.
“Ayyana ci gaba da amincewar INEC da NDC a matsayin abu da ya saba wa kundin tsarin mulki kuma haramtacce.
“Rushe ci gaba da amincewa da takardar rajistar NDC da INEC ta bayar;
“Ta hana INEC ci gaba da mu’amala da NDC a matsayin jam’iyyar siyasa; ta hana NDC ci gaba da bayyana kanta ko shiga kowace harkar zabe a matsayin jam’iyyar siyasa mai rajista.
“Na shigar da wannan kara ne ni kadai a matsayin dan kasa domin bunkasa bin kundin tsarin mulki, doka da kuma sahihancin tsarin zabe a dimokuradiyyarmu. Ba a yi ta a kan wani mutum ko wata kungiya ba.”

ADC na zawarcin jigon NDC

A wani labarin, mun kawo muku cewa ana rade-radin cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta fara zawarcin jigon NDC a Kano, Nasiru Gawuna.

Kara karanta wannan

"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Ana rade-radin cewa ADC ta masa alkawarin ba shi tikitin takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2027 idan ya sauya sheka zuwa cikinta.

Nasiru Gawuna ya koma NDC tare da haduwa da Rabiu Musa Kwankwaso ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng