Yadda za a Sabunta Fadar Sarkin Gombe Ta Zama Ta Yi Zarra a Arewa
- Gwamnatin Gombe ta amince da sake ginawa da inganta Fadar Sarkin Gombe domin ƙarfafa al'adun gargajiya da martabar masarautar
- Aikin zai samar da wuraren gudanar da bukukuwan al'adu, addini, taruka da sauran ayyukan gargajiya tare da kare tarihin masarautar Gombe
- Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ƙarfafa cibiyoyin gargajiya na daga cikin matakan tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Gwamnatin Jihar Gombe ta fara ɗaukar matakan sake ginawa da inganta Fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, CFR.
Aikin zai ƙara wa masarautar wuraren da suka dace da ayyukan al'adu, addini, bukukuwa da sauran harkokin gargajiya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da matakin da aka dauka ne a wani sako da mai magana da yawun gwamnan Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.
An fara shirin aiwatar da aikin
Matakin ya biyo bayan amincewar da aka bayar a taron majalisar zartarwar jihar, wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.
An tabbatar da cewa an kusa fara aikin bayan shugaban JPDESA, Mahmoud Yusuf, PhD, ya gabatar da takardar bayar da kwangilar aikin ga ɗan kwangila.
An bai wa kamfanin gine-gine na Datum kwangilar aikin, yayin da kamfanin Multy zai kasance mai ba da shawara kan aikin.
Abin da sabon aikin zai ƙunsa
Rahoto ya nuna cewa sake gina fadar zai ƙunshi gine-gine da wurare daban-daban da suka dace da matsayin masarautar gargajiya ta zamani.
Za a samar da wuraren gudanar da bukukuwan al'adu, ayyukan addini, tarukan sarauta da sauran muhimman harkokin gargajiya.
Aikin zai kuma yi ƙoƙarin kare tarihin masarautar, tsarin gine-ginen gargajiya da kimar al'adun da Fadar Sarkin Gombe ke wakilta.
Zaman lafiya ne tushen cigaba
Gwamnatin ta ce ba za a iya samun cikakken ci gaba ba tare da zaman lafiya ba, domin hanyoyi, makarantu da harkokin kasuwanci ba za su iya samar da amfani yadda ya kamata ba idan babu tsaro.

Source: Facebook
Ta bayyana cewa duk wani mataki na ƙarfafa cibiyoyin da ke taimakawa wajen samar da zaman lafiya ya kamata a ɗauke shi a matsayin zuba jari kan ci gaban al'umma.
Sanarwar ta ce sabuwar Fadar Sarkin Gombe za ta kasance wani bangare na ƙoƙarin haɗa ci gaban zamani da kiyaye tarihi da al'adun jihar.
Ana matsawa Goje ya koma PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa ana matsa wa tsohon Gwamnan Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, lamba domin ya fice daga APC ya koma PDP tare da mara wa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar, Farfesa Ali Isa Pantami, baya a zaɓen 2027.
Tsohon Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo da ɗan takarar PDP sun shiga ƙoƙarin shawo kan Goje ya koma jam'iyyar bayan ya kasa samun tikitin APC na kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya.
Magoya bayan PDP na ganin cewa komawar magoya bayan Goje da abokan siyasarsa daga dukkan shiyyoyin sanatan jihar zuwa PDP za ta ƙara wa jam'iyyar damar samun nasara a zaɓen gwamna na Fabrairun 2027.
Asali: Legit.ng

