2027: Barazanar da Peter Obi, Kwankwaso Ke Fuskanta a Arewa Daga Yan Yankin
- Jam’iyyar NDC da takarar haɗin gwiwar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na fuskantar turjiya daga wasu daga yankin Arewa
- Wasu jiga-jigan Arewa sun ce har yanzu NDC ba ta samu karɓuwa sosai ba, yayin da ake yaɗa saƙonnin da ke sukar Obi da Kwankwaso
- Sai dai shugabannin NDC a wasu jihohin Arewa sun ce jam’iyyar na samun sababbin mambobi da yawa, tare da ƙara faɗaɗa tsarinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Peter Obi na fuskantar ƙalubale wajen neman goyon bayan wasu masu ruwa da tsaki da masu zaɓe a Arewacin Najeriya.
Majiyoyi sun ce Obi na neman takara ne domin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 wanda ya zabi Rabiu Kwankwaso ke zama mataimakinsa.

Source: Facebook
Matsalar tikitin Obi, Kwankwaso a Arewa
Binciken Punch ya nuna cewa wasu shugabannin Arewa da masu sharhi kan siyasa sun bayyana cewa mafi yawan al’ummar yankin ba su rungumi jam’iyyar NDC ba tukuna.
An kuma ruwaito cewa wasu shugabannin yankin sun fara gargaɗin mabiyansu game da jam’iyyar, tare da bayyana Obi da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, a matsayin masu adawa da muradun Arewa.
A wasu saƙonnin siyasa da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, musamman WhatsApp, an bayyana haɗakar Obi da Kwankwaso a matsayin abin da bai dace ba ga yankin.
Haka kuma, an ruwaito cewa wasu fusatattun matasa sun ƙona fastocin yaƙin neman zaɓen Obi da Kwankwaso a ƙaramar hukumar Ungogo ta Kano.

Source: Twitter
Kungiyar ACF ta magantu kan tikitin Obi, Kwankwaso
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Arewa Consultative Forum, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya ce NDC har yanzu ba ta da cikakkiyar karɓuwa ko shahara a tsakanin talakawan Arewa.
Ya bayyana cewa duk da samun kulawar kafafen yaɗa labarai daga wasu fitattun ’yan adawa, har yanzu tasirinsu a Arewa ba shi da tabbas.
Muhammad-Baba ya kuma nuna shakku kan ƙarfin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa har ma ikon da yake da shi a Kano na iya raguwa idan aka kwatanta da shekarar 2023.
Martanin shugabannin NDC a Arewa
Sai dai wasu shugabannin NDC da masu nazarin siyasa sun musanta cewa jam’iyyar ba ta da karɓuwa a Arewa.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
Shugaban NDC na Borno, Haruna Amuda, ya ce jam’iyyar na samun ɗumbin masu sauya sheƙa daga wasu jam’iyyun adawa, musamman ADC.
A Jigawa kuma, wani jigo na jam’iyyar, Abdulrazak Birnin-Kudu, ya ce sun kafa masu gudanar da aiki a dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Ya bayyana matasa a matsayin ginshiƙin yaɗa manufofin jam’iyyar, yana mai cewa da yawa daga cikinsu sun gaji da tsohuwar siyasa.
An fara samun matsala a tikitn Obi, Kwankwaso
Mun ba ku labarin cewa matasan Arewa sun fara kalubalantar jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso kan kawancen da ya kulla da Peter Obi.
Wata kungiyar matasa ta soki shirun Kwankwaso kan zargin cin mutuncin da magoya bayan Obi suka yi wa Sardaunan Sokoto da Dan Fodio.
Ta ce alamu sun nuna cewa kawancen Obi da Kwankwaso ya fi karkata ga biyan bukatun siyasa da neman mulki fiye da kare muradun Arewa.
Asali: Legit.ng
