‘Darusan da Jam’iyyun ADC da NDC Ke Koya daga Jam’iyyar APC Mai Mulki’

‘Darusan da Jam’iyyun ADC da NDC Ke Koya daga Jam’iyyar APC Mai Mulki’

  • Jam’iyyar APC a Najeriya ta bugi kirji game da ci gaban da take samu musamman daga tsarin dimukradiyyar cikin gida
  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar ta zama abin koyi saboda gaskiya da adalci a zabukan cikin gida
  • Jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Montgomery, ya ce kasarsa za ta tura masu sa ido domin bibiyar zabukan gwamnoni na Ekiti da Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana tsarin dimukradiyyar jam'iyyar a matsayin abin koyi.

Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyun adawa da suka hada da ADC da NDC suna koyon darussa daga tsarin dimokuradiyyar cikin gida na jam’iyyarsa.

APC ta ce sauran jam'iyyu na koyar darussa a gare ta
Shugaban APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda da dandazon yan jam'iyyar a kasar. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Yilwatda ya bayyana haka ne a Abuja yayin wata ziyarar girmamawa da Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dakta Richard Montgomery, ya kai hedikwatar APC, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

'Zaben Peter Obi da Kwankwaso kamar ba Tinubu damar nasara ne a 2027'

'APC ta zama abin koyi ga sauran jam'iyyu'

Ya ce APC ta zama abin koyi ga sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya saboda jajircewarta wajen tabbatar da dimokuradiyya ta cikin gida da kuma gudanar da zabuka cikin gaskiya.

A cewarsa:

“Mu ne abin koyi ga sauran jam’iyyun siyasa. Suna bibiyar yadda muke gudanar da al’amura kuma sau da yawa suna kwaikwayon sababbin tsare-tsarenmu.”

Ya kara da cewa wannan matsayi yana dora wa APC babban nauyi na ci gaba da kafa ingantattun ka’idoji a harkokin siyasa da dimokuradiyyar cikin gida.

APC ta fadi nasarar da aka samu a zaben fitar da gwani
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Nasarar APC a zabukan fitar da gwani

Yilwatda ya yi nuni da zabukan fitar da gwani na baya-bayan nan da jam’iyyar ta gudanar, ya ce sama da mambobi 6,000 suka shiga, kuma kasa da kashi uku cikin dari ne suka gabatar da koke.

A cewarsa, karancin korafe-korafen ya nuna cewa zabukan sun kasance cikin lumana, gaskiya da kuma karbuwa ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Ya kuma sake jaddada kudirin APC na tabbatar da zaman lafiya a zabukan gwamnonin Ekiti da Osun, yana mai cewa jam’iyyar za ta mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci maimakon amfani da son rai.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Hakeem Baba Ahmed ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi murabus

Tun da farko, Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dakta Richard Montgomery, ya bayyana cewa kasarsa za ta tura tawagogin masu sa ido domin bibiyar zabukan gwamnonin jihohin biyu, cewar Punch.

Montgomery ya ce zabukan na da muhimmanci domin su ne zabukan gwamnoni na karshe da za a gudanar kafin babban zaben kasa na shekara mai zuwa.

Yilwatda ya kuma yabawa sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa gwamnati na kokarin gina tattalin arziki mai karfi da fadada muhimman ayyukan more rayuwa.

APC ta kausasa harshe kan hare-hare

Mun ba ku labarin cewa 'Yan ta'adda sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yayin wasu hare-hare da suka kai a jihar Niger.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi Allah da kashe-kashen da 'yan ta'addan suka yi.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa wadannan ayyukan na rashin imani ba abu ba ne wanda za a yarda da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.