2027: Matawalle Ya Fito Fili Ya Bayyana Kalar Zaben da Za a Yi a Karkashin Gwamnatin Tinubu
- Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ba 'yan Najeriya tabbataci kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Ministan ya ce Bola Tinubu ya nuna aniyarsa ta hana amfani da hukumomin gwamnati wajen tsoratar da ’yan adawa
- Kungiyar Tinubu Second Term Mandate ta ce tana fatan Tinubu ya samu aƙalla kashi 60 na ƙuri’un da za a kada a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna – Karamin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya yi magana kan irin zaben da za a gudanar a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bello Matawalle ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za a gudanar da babban zaɓen 2027 cikin ’yanci, adalci da sahihanci a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Matawalle, wanda Dr Auwal Abdullahi ya wakilta, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan Tinubu Again Movement da sauran ƙungiyoyin siyasa da suka taru a Kaduna, cewar rahoton Daily Trust.
Kungiyoyin sun taru ne domin wayar da kan jama’a da neman goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasar.
Matawalle ya ce Shugaba Tinubu ya nuna aniyar siyasa wajen tabbatar da cewa an samar da daidaito ga dukkan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.
Tinubu ba zai tsoratar da ’yan adawa ba
A cewarsa, salon shugabancin Tinubu ya nuna cewa yana da niyyar hana amfani da hukumomin gwamnati wajen tsoratar da jam’iyyun adawa.
Matawalle ya ce shugaban ya bayar da umarnin a cire takunkumin da aka sanya wa wani asusu saboda gabatowar zaɓe, yana mai cewa hakan ya nuna cewa Tinubu ba ya son katsalandan a harkokin siyasa.
Ya kuma ce Tinubu ya bayyana a fili cewa babu wanda ya kamata ya yi amfani da sunansa ko matsayinsa na gwamnati wajen tsoratar da ’yan adawa.
Matawalle ya bayyana Tinubu a matsayin ɗan siyasar da ya taso daga tushe har zuwa fadar shugaban ƙasa bayan shafe shekaru yana shiga harkokin siyasa tare da samun gogewa.

Kara karanta wannan
Babban Sarki ya kama layi, ya ce ya kamata a hana kowa kamfe a jihar ban da Tinubu
Ya ce: “Zan iya tabbatar muku, bisa kalamansa, cewa zaɓen 2027 zai kasance cikin adalci da sahihanci. Amma zan iya tabbatar muku cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaɓen.”
Ƙungiyoyi na shiga Tinubu Again Movement
Ministan ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin siyasa masu goyon baya a faɗin ƙasar da su shiga Tinubu Again Movement, yana mai bayyana kungiyar a matsayin wani dandali na ƙasa da aka kafa domin ganin Tinubu ya sake samun nasara a zaɓen 2027.
Ya ce ba don biyan bukatun wasu mutane aka kafa ƙungiyar ba, illa dai domin tattara ’yan Najeriya da neman goyon bayansu ga burin shugaban ƙasa na 2027.
Matawalle ya ce ƙarin ƙungiyoyin siyasa masu goyon baya na shirin shiga tafiyar, yana kwatanta yunƙurin wayar da kan jama’ar da cewa jirgin ƙasa ne da ke tafiya wanda zai kai Tinubu ga nasara a 2027.

Source: Original
Abin da Matawalle ya ce kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa Allah ne kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
Ministan ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa da kowa ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ba, don haka ya kamata 'yan Najeriya su haɗa kai da jami'an tsaro domin kawo ƙarshenta.
Asali: Legit.ng
