Kotu Ta Dakatar da Shari'ar da Aka Nemi Soke Rijistar ADC da Wasu Jam'iyyun Siyasa a Najeriya
- Babbar kotun tarayya ta dage shari'ar neman soke rijistar ADC da wasu jam'iyyu fiye da hudu har sai baba ta gani
- Rahoto ya nuna cewa kotu ta dauki wannan mataki ne bayan samun umarni daga kotun daukaka kara na dakatar da shari'ar gaba daya
- Masu kara sun nuna damuwa bisa dakatar da shari'ar bayan ta kai matakin yanke hukunci, sun ce ba za su hakura ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage ci gaba da shari’ar da ke neman a soke rajistar jam’iyyun siyasa da suka hada da ADC, Accord Party da AA har sai baba ta gani.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Peter Lifu, ya sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci a shari’ar da wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ta shigar.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Abubuwa 4 da 'yan ta'adda suka nema kafin su sako dalibai da malaman Oyo

Source: Twitter
Sai dai Daily Trust ta rahoto cewa an samu tsaiko a shari’ar ne bayan da jam’iyyar Accord Party ta samu umarnin dakatar da ci gaba da shari’ar daga Kotun Daukaka Kara a ranar 29 ga watan Mayu.
Kotu ta dakatar da yanke hukunci
A farkon zaman kotun jiya Juma'a, ma’aikacin kotu ya sanar da bangarorin da ke shari’ar cewa an dage yanke hukuncin, kuma za a sanar da sabon lokaci daga baya.
Wannan mataki ya sa aka dakatar da dukkan shari’ar ba tare da an yanke hukunci ba.
Shugaban kungiyar da ta shigar da karar, Mista Raphael Igbokwe, ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin Kotun Daukaka Kara na bayar da umarnin dakatar da shari’ar.
Masu kara sun yi fatali da matakin
Ya ce matakin ya jawo cikas ga shari’ar da ta riga ta kai matakin yanke hukunci, in da ya tabbatar da cewa kungiyarsu ta riga ta daukaka kara zuwa Kotun Koli kan umarnin dakatar da shari’ar.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano
Ya ce:
“Muna cikin damuwa cewa shari’ar da ta kai matakin yanke hukunci yanzu an dakatar da ita, a zahiri, hakan tamkar aan dakile adalci ne.”
Ya kara da cewa kungiyar za ta ci gaba da bin dukkan hanyoyin doka domin tabbatar da an warware batun cikin adalci, domin karfafa dimokuradiyya a Najeriya.
Jam’iyyun da ake neman rushe su
Rahoton tashar channels ya nunana cewa shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026 ta shafi Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a matsayin wacce ake kara ta farko.
A cikin wadanda ake kara akwai jam’iyyu da dama ciki har da ADC, AA, APP, Accord Party da ZLP da sauransu.
Babachir Lawal ya fice daga ADC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC a hukumance.
Babachir Lawal ya kuma yi zargin cewa zaɓukan fitar da gwani da jam’iyyar ADC ta gudanar sun kasance cike da magudi da rashin adalci.
Ya ce abin da ya gani yayin gudanar da zaɓen fitar gwani ya sa ya rasa amincewa da tsarin dimokuraɗiyyar cikin gida na jam’iyyar ADC
Asali: Legit.ng