Jihar Bauchi
Sanata Abdul’aziz Yari ya gargadi ’yan Arewa kan dagewa da neman shugabancin Najeriya, yana cewa raba mulki tsakanin yankuna na taimakawa haɗin kan ƙasa.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kare Sanata Shehu Buba Umar zargin da ake yi masa na alaka da ta'addanci inda ya ce yaba masa kan kokarin da yake yi.
Jam'iyyar PRP ta kare Sanata Shehu Buba kan zargin alakarsa da ‘yan bindiga, tana mai cewa ƙaryace aka shirya domin bata masa suna gabanin zaɓen 2027.
APC na fuskantar sabon rikici a Bauchi bayan wasu yan takarar majalisar dokokin jihar sun zargi jam’iyyar da sauya sunayensu bayan sun yi nasara a zaɓen fidda gwani.
Jami’in NDLEA ya rasa ransa bayan an caka masa wuka a jihar Bauchi yayin da hukumar ta ayyana wanda ake zargi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Mataimakin Sanata Shehu Buba a bangaren majalisa, Abba Aliyu Tilde, ya yi murabus yayin da ake sabunta zarge-zargen alakanta sanatan da ’yan bindiga.
APC Youth Parliament ta shirya ɗaukar nauyin karatun yara 60 marasa galihu na shekara guda domin murnar cikar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shekaru 60.
Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi Sagir Saleh da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun fice daga jam’iyyar, suna zargin rashin adalci da tilasta ‘yan takara.
Sanata Shehu Buba ya musanta daukar nauyin ’yan bindiga, yana mai cewa bidiyoyin da ake yadawa kansa na bogi ne, yayin da ya ce zai kare mutuncinsa ta doka.
Jihar Bauchi
Samu kari