Zaben Fitar da Gwanin APC Ya Bar Baya da Kura, an Fara Neman Hanyar Gyara
- Gwamna Hope Uzodimma ya shawarci mambobin APC su haɗa kai bayan zaɓen fitar da gwani da ya tayar da rigima
- Uzodimma ya ce siyasa hidima ce ga jama'a, ba neman biyan bukatun kai ba, tare da yaba nasarar zaɓukan cikin gida da aka gudanar
- Shugabannin APC da tsofaffin masu neman takara sun yaba da gaskiya da adalcin zaɓen fitar da gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owerri, Imo - Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar APC a jihar da su rungumi sulhu da haɗin kai bayan kammala zaɓen fitar da gwani.
Hakan ya biyo bayan rikice-rikice da aka samu bayan sanar da sakamakon fitar da gwani da aka gudanar a fadin kasar baki daya.

Source: Facebook
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a cibiyar taro ta Emmanuel Iwuanyanwu da ke Owerri, Uzodimma ya bukaci masu neman takara, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
2027: Babachir Lawal ya rikita lissafin Atiku Abubakar, ya fice daga jam'iyyar ADC
Uzodinma ya shawarci mambobin APC a Imo
Ya ce waɗanda ba su yi nasara ba su rungumi kaddara tare da ci gaba da kasancewa masu biyayya ga jam’iyya domin cimma manufofinta.
Uzodimma ya ce babu yadda za a samar da maslaha ba tare da sadaukarwa ba, yana mai cewa siyasa hidima ce ga jama'a.
Gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, gaskiya, da bunƙasar tattalin arziki mai anfani ga kowa a jihar.
Ya kuma yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa ci gaban Imo tare da kira ga rajistar masu zaɓe.
Uzodimma ya ce:
“Ƙarfin jam’iyyarmu shi ne ƙarfinku. Mu haɗa kai, mu jure wa juna, mu yi aiki tare domin samun nasara.”

Source: Facebook
Shugaban APC ya yabawa mambobin jam'iyyar
Tun da farko, shugaban APC na Imo, Austin Onyedebelu, ya yaba da yadda mambobin jam’iyyar suka gudanar da kansu cikin lumana yayin zaɓen fitar da gwani.

Kara karanta wannan
"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027
Ya ce an gudanar da zaɓen kai tsaye na ‘yan takarar majalisu da shugaban ƙasa ba tare da samun rahoton tashin hankali ko rikici ba.
Onyedebelu ya danganta nasarar zaɓen ga shugabancin Gwamna Uzodimma, yana mai cewa ya samar da yanayin da ya ba da dama.
Ya kuma bukaci waɗanda suka yi nasara su kasance masu tawali’u, yayin da ya ƙarfafa waɗanda suka fadi zaɓe kada su rasa su.
Tsofaffin masu neman tikitin majalisar dokoki da dattawan jam’iyya daga yankunan sanatoci uku sun sake jaddada biyayyarsu ga APC, cewar Daily Post.
Tsohon minista ya shawarci masoyansa kan barin APC
A baya, kun ji cewa tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi magana kan zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a jihar Oyo.
Adebayo Adelabu ya nuna cewa har yanzu uwar jam'iyya ta kasa ba ta sanar da sakamakon zaben ba a hukumance.
Tsohon ministan ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar da ka da su fice daga cikinta inda ya nuna cewa hakan bai kamata ba.
Asali: Legit.ng