
Jihar Oyo







Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana sanyawa masallaci sunan gwamna Makinde na jihar, inda MURIC ta ce sam hakan bai dace ba kuma dole a gaggauta sauya sunan nasa.

Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta koma bayan ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Oyo. Jam'iyyar na son a kawar da mulkin gwamnan PDP a jihar.

Tsohon dan majalisar dokokin jihar Oyo wanda ya wakilci mazabar Ido, Tirimisiyu Okunola, ya rasu a ranar Lahadi, 5 ga watan Maris bayan yayi fama da ciwon siga.

Gamayyar wasu kungiyoyin magoya bayan zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a kudu maso yammacin Najeriya sun ayhana goyon baya ga tazarcen Makinde.

Rahoto ya ce wata ‘yar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce babu wata yarjejeniya da ya ajiye da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Magoya bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo, sun koma bayan ɗan takarar gwamnan APC a jihar. An dai kusa a fara zaɓen gwamnoni a Najeriya.
Jihar Oyo
Samu kari