2027: Atiku da Manyan ADC za Su San Makomarsu game da Takarar Shugaban Kasa

2027: Atiku da Manyan ADC za Su San Makomarsu game da Takarar Shugaban Kasa

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da Rotimi Amaechi za su fafata a zaɓen fitar da da gwani na ADC ranar Litinin 25 ga watan Mayu, 2026
  • Haka haka nan masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen na neman girgiza manyan ‘yan siyasar jam’iyyar a takarar shugaban ƙasa da za a tu
  • Shugabannin ADC sun ce an kammala shirye-shirye domin gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani kafin zaɓen 2027 yayin da sauran jam'iyyu ke shiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da masanin tattalin arziki, Mohammed Hayatu-Deen, za su gwabza a yau.

Dukkaninsu za su fafata a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, 2026 gabanin babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

ADC ta fitar da sanarwa, Atiku na shirin fafatawa da masu neman takarar 2027

Atiku da sauran yan takara za su fafata a yau
Atiku Abubakar Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen Hoto: Atiku/Victor Burubo/Mohammed Hayatu-deen
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ana sa ran zaɓen zai kasance mai zafi yayin da kowannensu ke neman zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar gabanin shekarar 2027.

ADC za ta yi zaben fitar da gwani

Jaridar Punch ta ruwaito cewa rahotanni daga cikin jam’iyyar sun nuna cewa an kasa cimma matsaya tsakanin manyan masu neman takarar.

Wannan al'amarin da ya sa shugabancin jam'iyyar ADC ya amince da zaɓe domin tantance wanda zai ɗaga tutar jam’iyyar ya tunkari zaben 2027.

Masu neman takarar sun samu damar shiga fafatawar ne bayan kammala tantance su da kwamitin da tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke, ya jagoranta.

An so sasanta yan takara a ADC

Shugaban riƙo na jam’iyyar ADC, David Mark, ya jagoranci yunkurin sasanta ‘yan takarar domin a samu ɗan takara ta hanyar maslaha, amma hakan bai yi nasara ba.

Domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, jam’iyyar ta kafa kwamitin zaɓen shugaban ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

Farfesa Yisa Gana ne zai kasance sakataren kwamitin, yayin da sauran 'yan jam'iyya suka haɗa da Manjo Janar Adamu Jalingo, Dakta Auwalu Anwar, Cif Emenike Ikechi da Dakta Macaulay Iyare.

Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa an kammala shirin zabe
Bolaji Abdullahi, kakakinjam'iyyar ADC ta kasa Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Sauran sun hada da Tajudeen Bakare, Elder Ubolo Itodo Okpanachi, Zainab Buba Galadima, Uzoamaka Onyeama da Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris.

Hakazalika, ADC ta kafa kwamitin ɗaukaka ƙara ƙarƙashin jagorancin Dakta Suleiman Usman (SAN), yayin da Barista Ken Imasuagbon zai kasance sakatare, sai Barrister Dare Okerade a matsayin mamba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa an tura jami’an zaɓe zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

ADC ta fitar ta ssanarwa

A wani labarin, mun wallafa cewa jam’iyyar ADC ta bukaci masu neman takarar shugaban kasa, shugabannin jam’iyya da mambobinta su bayar da hadin kai gabanin zaben fitar da gwani.

Hakan na zuwa ne yayin da Atiku Abubakar da wasu 'yan takara biyu za su fafata a zaben fitar da gwani na jam'iyyar a yau Litinin, 25 ga Mayun 2026 domin tantance waye zai zama wakilin jam'iyyar.

Sakataren yada labaran jam'iyyar hamayya ta ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana zaben fitar da gwanin a matsayin wani muhimmin lokaci ga jam’iyyar da kuma ‘yan Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng