'Mutumina ne': Peter Obi Ya Yi Magana da Ake Zargin Yana Gujewa Atiku
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi ya musanta zargin cewa yana guje wa Atiku Abubakar kafin zaben 2027
- Obi ya bayyana cewa Atiku babban jagora ne kuma dan uwansa na siyasa wanda ba zai bar shi domin wata buƙatarsa ba
- Tsohon gwamnan da Rabi'u Kwankwaso sun fice daga ADC zuwa NDC bayan rikice-rikicen cikin gida da shari’u da suka ce sun karkatar da hankalin jam’iyyar daga matsalolin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya yi magana game da alkarsa da Atiku Abubakar.
Obi ya musanta rade-radin cewa yana guje wa Atiku Abubakar gabanin zaben 2027 da ake tunkara bayan barin ADC zuwa NDC.

Source: UGC
Obi ya bayyana hakan ne a Cape Town na kasar Afirka ta Kudu yayin taron Spier Dialogue 2026, wanda ke tattauna harkokin shugabanci a Afirka, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci
Ya ce akwai mutane kalilan da suke da kusanci da shi kamar Atiku, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban kasar babban jagoransa ne kuma dan uwansa.
Obi ya ce bai taba gudun Atiku ko wani mutum ba, yana mai jaddada cewa salon tafiyar siyasarsa ne kawai ya bambanta da na wasu.
Kalaman nasa sun zo ne bayan watanni ana samun matsaloli da sabani a alakarsu ta siyasa kafin babban zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Tun farko dai Obi da Atiku sun amince da amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin hadaka domin kalubalantar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.

Source: Twitter
Yadda haduwar Obi da Atiku ta wargaje
A ranar 1 ga Janairu, 2026, Obi ya shiga ADC a hukumance, inda Atiku ya yaba da matakin tare da bayyana shi a matsayin babban ci gaba.
Sai dai hadakar tasu ba ta dore ba, domin daga baya Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar saboda rikice-rikicen cikin gida da shari’u masu yawan gaske.
Obi ya bayyana cewa matsalolin cikin gida sun hana jam’iyyar mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban Najeriya da walwalar al’umma.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa
Daga baya, Obi da Rabiu Kwankwaso suka koma jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, inda suka bukaci kawo karshen siyasar dogaro da kararrakin kotu.
Obi ya bayyana cewa matsalolin cikin gida sun hana jam’iyyar mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban Najeriya da walwalar al’umma.
Daga baya, Obi da Rabiu Kwankwaso suka koma jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, inda suka bukaci kawo karshen siyasar dogaro da kararrakin kotu.
Fasto ya yi hasashen nasarar Peter Obi
Mun ba ku labarin cewa wani fitaccen malamin addini na ƙasar Ghana ya yi hasashen cewa Peter Obi yana da gagarumar dama ta samun shugabancin Najeriya a shekarar 2027.
Fasto Clement Testimony ya bayyana sharuɗɗa guda uku da dole ne Obi ya cika su domin tabbatar da burinsa na zama shugaban ƙasa.
An ba Obi shawarar da ya ziyarci Shugaba John Dramani Mahama a ƙasar Ghana a matsayin wani ɓangare na cika burinsa.
Asali: Legit.ng