Ministan da Ya Ajiye Aiki Ya Yi Biyu Babu wajen Neman Takarar Gwamna a APC
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta gudanar da zaben fitar gwani na masu neman takarar gwamna a jihar Oyo
- 'Yan takarar da suka shiga zaben fitar da gwanin sun fafata, inda daga karshe sanata mai wakiltar Oyo ta Kudu ya yi nasara
- Sanata Sharafadeen Alli ya samu nasarar ne bayan doke abokan hamayyarsa ciki har da tsohon Ministan lantarki, Adebayo Adelabu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Sanata mai wakiltar Oyo ta Kudu a Majalisar dattawa, Sharafadeen Alli, ya lashe zaɓen fitar da gwani na takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo.
Sanata Sharafadeen Alli ya samu nasarar ne bayan ya fafata da 'yan takara, ciki har da tsohon Ministan lantarki, Bayo Adelabu.

Source: Twitter
Sharafadeen Alli ya zama dan takarar APC
Jaridar Leadership ta kawo rahoton nasarar da sanatan ya samu a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayun 2026.
Sharafadeen Alli, wanda ya samu ƙuri’u 578,143, Sanata Abdulfatai Buhari ne ya biyo bayansa da ƙuri’u 37,265, yayin da tsohon Ministan lantarki, Oloye Bayo Adelabu, ya samu ƙuri’u 19,193.
Tsohon Minista ya yi korafi
A halin da ake ciki, ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan a inuwar APC, Adebayo Adelabu, ya nuna damuwa kan zargin tafka kura-kurai a lokacin zaɓen fitar da gwani na gwamna na jam’iyyar da aka gudanar a faɗin jihar.
Yayin da yake magana da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’a a mazaɓa ta 9, karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas, Adelabu ya bayyana zaben a mazaɓarsa da cewa na zaman lafiya ne, inda ya lura cewa ya samu gagarumin goyon baya daga mambobin jam’iyyar a yankin.
A cewarsa, daga cikin kimanin mambobin jam’iyyar 437 da suka yi rajista a mazaɓar, fiye da 430 ne suka kaɗa ƙuri’a don nuna goyon baya gare shi, rahoton Channels tv ya nuna hakan.
“Wannan shi ne gidan kakannina kuma mazaɓata. Na gamsu da abin da muka shaida a nan yau. Tsarin ya kasance na zaman lafiya da adalci ba tare da wani tashin hankali ko tsoratarwa ba."

Kara karanta wannan
Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye
- Adebayo Adelabu

Source: Twitter
Adelabu ya yi zargin aikata ba daidai ba
Sai dai kuma, jigon na APC ya yi zargin cewa rahotanni daga mazaɓu da dama a faɗin jihar sun nuna jerin matsaloli na ba daidai ba wajen zaɓe, tsoratarwa, da kuma karkatar da sakamako.
Adelabu ya yi iƙirarin cewa a wasu mazaɓun, an gudanar da zaɓubbukan ne kafin lokacin da aka tsara, yayin da a wasu kuma, an hana mambobin jam’iyyar kaɗa ƙuri’a ta hanyar tsoratarwa da tashin hankali.
“A wasu wuraren, ba a ma gudanar da zaɓubbukan ba sam, amma an yi zargin cewa an rubuta sakamakon sannan aka ajiye su. Wannan ba abu ba ne mai kyau ga dimokuraɗiyyarmu, kuma dole ne a yi wani abu a kai."
- Adebayo Adelabu
Gwamna Abba ya samu tikitin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben 2027.
Jam’iyyar APC a jihar Kano ta zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takararta na maslaha domin zaben 2027 da ake tunkara.
APC mai mulki ta zabi Alhaji Abba Kabir Yusuf ne a matsayin dan takarar gwamnan Kano gabanin babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

