Tsohon Gwamna Ya Juyawa Atiku Baya, Ya Ce ba Ya Son Ɗan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa a 2027

Tsohon Gwamna Ya Juyawa Atiku Baya, Ya Ce ba Ya Son Ɗan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce ba zai goyi bayan Atiku Abubakar ko wani ɗan Arewa ba a zaben 2027
  • Samuel Ortom ya ce har yanzu yana goyon bayan tsarin karba-karba, wanda ya mika mulki zuwa yankin Kudancin Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana tare da Shugaba Bola Tinubu da Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba shi da wani dalili ko shirin goyon bayan dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar.

Ortom ya jaddada cewa ba zai goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ko wani dan takarar shugaban kasa daga Arewa a babban zaben 2027 ba.

Samuel Ortom.
Tsohon gwamnan jihar Benue da ke Arewa ta Tsskiya, Samuel Ortom Hoto: Samuel Ortom
Source: Facebook

A rahoton Leadership, Ortom ya ce har yanzu yana nan kan matsayinsa na ganin cewa shugabancin Najeriya ya kamata ya ci gaba da kasancewa a Kudu a 2027.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10 kafin a fara kamfen, sabani ya shiga tsakanin Atiku da ADC

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, yayin da ake tunkarar babban zaben.

Ortom ya musanta goyon bayan Atiku

Wata kungiya ta yi ikirarin cewa Ortom na cikin wata yarjejeniya ta goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a zaben shugaban kasa na 2027.

Sai dai Ortom, ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Zege Paul Terhide, ya musanta ikirarin, yana mai bayyana shi a matsayin karya, mara tushe kuma wanda ya saba wa matsayarsa.

Terhide ya ce matsayar Ortom kan wanda ya kamata ya jagoranci Najeriya ba ta canza ba, har yanzu ya yi imanin Kudu ya kamata ta ci gaba da mulki.

Ortom ya tuna matsayar tawagar G-5

A cewar sanarwar, a lokacin kakar zaben 2023, Ortom da gwamnonin PDP hudu da suka hada G-5, sun tsaya kan cewa bayan shekaru takwas na Muhammadu Buhari daga Arewa, adalci da hadin kan kasa sun bukaci a mayar da shugabancin Najeriya zuwa Kudu.

Kara karanta wannan

Saƙon da Bola Tinubu ya tura wa 'yan ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya da wasu ƙasashe

Sanarwar ta ce matsayar G-5 ba ta samo asali daga kiyayya da wani dan siyasa ba, illa dai imanin cewa manyan sassan Najeriya su samu damar jin cewa suna da wakilci a shugabancin kasar.

Ortom ya kasance daya daga cikin masu tsayawa kan wannan matsaya duk da irin matsin lambar siyasa da ya fuskanta a lokacin.

Shin Ortom ya canza shawara ne?

Terhide ya ce Ortom har yanzu yana ganin cewa ka’idar da ta jagoranci matsayar G-5 a 2023 tana da muhimmanci a gabanin zaben 2027.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar lokacin da ya karvi bakuncin magoya bayansa a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cewarsa, bayan goyon bayan mayar da shugabancin kasar zuwa Kudu bayan shekaru takwas na mulkin Arewa, Ortom ba zai ya sauya matsayinsa ya goyi bayan dan Arewa ba.

Sanarwar ta ce:

“Har yanzu Ortom ya yi imani cewa ka’idar da ta jagoranci matsayar G-5 a 2023 tana nan daram a gabanin zaben shugaban kasa na 2027.”

Wike ya soki Atiku da Peter Obi

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce tikitin Atiku/Amaechi da Obi/Kwankwaso ba za su iya kayar da Tinubu da Shettima a zaɓen 2027 ba.

Tsohon gwamnan Ribas ya ce Tinubu ya nuna jarumtar siyasa da.gwamnatocin baya suka kasa nunawa, musamman wajen kawo karshen tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262