Tinubu Ya Yi Karin Haske kan Zargin Shirin Sauya Sunan Najeriya, Rusa Shari'ar Musulunci
- Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin da ke yawo cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya sunan Najeriya
- Sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ƙaryata maganar sauya sunan kasar zuwa “United States of Nigeria” tare da soke dokar Shari’a a Arewa
- Ta ce rahoton karya da ya bazu a kafafen sada zumunta na dauke da bayanan bogi daga wasu majiyoyi marasa tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar shugaban kasar ta yi ƙarin haske kan jita-jitar shugaban kasa, Bola Tinubu na shirin sauya sunan Najeriya.
Fadar ta jaddada cewa yin gyaran kundin tsarin mulki babban aiki ne da ke bukatar amincewar kaso biyu bisa uku na majalisar tarayya da kuma majalisun jihohi 24.

Source: Twitter
Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.
Abin da Tinubu ya mayar da hankali kai
Onanuga ya ce gwamnatin Tinubu tana mayar da hankali ne wajen karfafa gyaran tattalin arziki da samar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya maimakon shiga batutuwan da za su haddasa rikici.
Ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su guji yada ko amincewa da rahotannin karya da ke neman haddasa rudani yayin da yakin neman zaben 2026 ke kara karatowa.
Fadar shugaban kasar ta bayyana masu yada irin wadannan labarai a matsayin masu neman tayar da zaune tsaye da rikicin siyasa a kasar.
Tinubu ya yi magana kan shari'ar Musulunci a Arewa
Tinubu ya ce babu wani shiri na soke Shari’a ko sauya tsarin kasar, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Rahoton karya ya haddasa ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kafin Fadar shugaban kasa ta fito fili ta karyata dukkan ikirarin da aka yada.
Akwai gargadin cewa rahotannin karya da raba kan jama’a na iya karuwa yayin da kasar ke shirin gudanar da zabukan shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa
Fadar shugaban kasa ta bukaci jama’a su rika tantance bayanai daga sahihan hanyoyi domin kauce wa fadawa tarkon masu yada labaran bogi.
Rahoton ya kara jaddada cewa duk wani sauyi ga kundin tsarin mulki dole ne ya bi matakan doka da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya.
Onanuga ya ce masu yada labaran karya suna amfani da siyasa wajen kokarin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a a Najeriya.
Fadar shugaban kasa ta bukaci kafafen yada labarai da masu amfani da sada zumunta su tabbatar da gaskiyar bayanai kafin yadawa.
Tinubu ya magantu kan matsalar tsaro
A wani labarin, an ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa mutanen da ke da hannu wajen matsalar rashin tsaro na yi masa fatan mutuwa.
Ya nuna cewa akwai mutanen da ya bakantawa rai sakamakon manufofin gwamnatinsa, inda suke son daukar ramuwar gayya.
Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro wadda ta addabi sassa da dama na kasar mai arzikin man fetur.
Asali: Legit.ng
