Ana Shirin Babbar Salla, ’Yan Bindiga Sun Yi Fashin Ragunan Layya a Kano

Ana Shirin Babbar Salla, ’Yan Bindiga Sun Yi Fashin Ragunan Layya a Kano

  • Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun tare dillalan dabbobi daga Kano tare da sace ragunansu da suka tana da saboda shirin babbar salla
  • Daya daga cikinsu ya ce maharan sun iso da mota, suka harba bindiga sama sannan suka tilasta musu kwanciya kafin satar dabbobin
  • Lamarin ya sake nuna yadda matsalar tsaro ke barazana ga matafiya da ‘yan kasuwa musamman yayin da ake shirin kasuwar Babbar Sallah a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ajingi, Kano - A daren Laraba 20 ga watan Mayun 2026 wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari kan wasu dillalan dabbobi ana shirin bikin salla.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa mutane da suka fito daga jihar Kano sun gamu da maharan ne a kan hanyarsu ta zuwa Kogi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Yan bindiga sun sace raguna a Kano
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yamma. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni daga shafin Bakatsina a X sun bayyana cewa maharan sun sace raguna guda 11 yayin da ‘yan kasuwar ke hanyarsu ta zuwa Ankpa a Kogi domin kasuwanci.

Dillalan dabbobin daga Kano sun magantu kan lamarin

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Hamisu Abdu Sakalawa, ya bayyana cewa harin ya faru ne a ƙauyen Dakatsalle da ke Bebeji.

Ya ce suna jiran abin hawa ne domin ci gaba da tafiya lokacin da wasu mutane ɗauke da makamai suka iso cikin wata mota.

A cewarsa, maharan sun fara harba bindiga sama domin razana su sannan suka umurce su da su kwanta tare da rufe idanunsu.

Bayan haka, maharan sun tattara ragunan tare da tserewa daga wurin cikin gaggawa ba tare da wani ya iya hana su ba.

Daga baya dillalan dabbobin sun kai rahoton harin ga ofishin ‘yan sanda na Dakatsalle domin neman matakin tsaro da bincike.

Kara karanta wannan

Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu

Mutane da dama sun nuna damuwa cewa matsalar rashin tsaro ta kai matakin da hatta dillalan dabbobi ke fuskantar hare-hare kafin Babbar Sallah.

Yan bindiga sun yi fashin ragunan layya a Kano
Sufeta-janar na yan sandan Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Yadda hare-haren a jihar Kano ke kara kamari

Wasu masu sharhi sun ce miyagu na amfani da sunan ‘yan bindiga wajen aikata laifuka da tayar da hankalin jama’a a yankuna daban-daban.

Lamarin ya ƙara jefa fargaba tsakanin matafiya da ‘yan kasuwa masu amfani da manyan hanyoyin Najeriya domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da suka fara fuskantar hare-haren yan bindiga a baya bayan nan wanda yanzu ya zama ruwan dare a wasu yankunan kauyuka.

Ta'addanci: Matasa sun yi bore a Kano

Mun ba ku labarin cewa wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a jihar Kano domin jawo hankalin gwamnatin Abba Kabir Yusuf game da rashin tsaro.

Matasan sun fara zanga-zangar a matsayin ta lumana, amma daga baya lamarin ya rikide zuwa tashin hankali a karamar hukumar Gwarzo wanda ya jawo kona ginin gwamnati.

Zanga-zangar da suka yi ta biyo bayan karuwar ayyukan 'yan ta'adda da ake samu a Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo inda aka kashe mutum 2.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.