Bakin Sanatan APC Ya Jawo Masa, Gwaman Zai Yi Kararsa bayan Gindaya Sharuda
- Tawagar yakin neman zaben Gwamna Ademola Adeleke ta yi barazanar kai karar Sanata Francis Fadahunsi
- Lauyan Pelumi Olajengbesi ya bukaci Fadahunsi ya janye kalaman da ya yi tare da neman gafara a bainar jama’a cikin sa’o’i 24
- Lauyan ya ce idan Fadahunsi bai cika bukatar ba, za a garzaya kotu domin neman diyyar Naira biliyan 10 saboda bata suna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Kalaman sanatan APC da ya yi ana shirin zaben gwamnan Osun ya jawo masa matsala saboda cike suke da barazana.
Mai magana da yawun yakin neman zaben Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, Pelumi Olajengbesi, ya yi barazanar kai karar Sanata Francis Fadahunsi kan zargin bata suna da karya mai cutarwa.

Source: Twitter
A cikin wata wasika mai kwanan wata 12 ga Agustan 2026, lauyan Olajengbesi, Hammed Lasisi, ya bukaci sanatan ya janye wasu kalaman da ya yi, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: An tura saƙo ga Amurka da Birtaniya don su hukunci sanatan Najeriya
An soki kalaman barazana na sanatan APC
Olajengbesi ya bayyana kalaman Fadahunsi a matsayin miyagu da masu cutar da mutuncinsa, bayan hirarrakin da sanatan ya yi a gidajen talabijin.
An ce kalaman sun fito ne yayin wata hira kai tsaye da Fadahunsi ya yi a Viable TV ranar 2 ga Yulin 2026.
Haka kuma, an sake yin wasu kalamai yayin bayyanar sanatan a shirin Politics Today na Channels Television ranar 11 ga Agustan 2026.
A cewar wasikar, Fadahunsi ya yi kalaman da suka shafi asalin Olajengbesi, tare da zargin cewa yana amfani da ’yan daba da kungiyoyin asiri wajen gudanar da harkokin siyasarsa.
Lauyan ya ce irin wadannan kalamai sun sanya tambaya kan asalin Olajengbesi a matsayin dan Ijebu-Jesha, tare da alakanta shi da ayyukan kungiyoyin asiri.

Source: Original
Bukatar lauya ga sanatan APC
A wata hira da aka yi ranar 11 ga Agusta, Fadahunsi ya kuma alakanta marigayi Ajayi Aderogba, wanda aka fi sani da Rogba, da kungiyar Eiye.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Sheikh Jingir ya yi ƙarin bayani kan kalamansa da suka tayar da ƙura a Najeriya
Lauyan ya bukaci Fadahunsi ya janye kalaman da ake zargin ya yi, ta hanyar amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta da aka yada su.
Haka kuma, ya bukaci sanatan ya gabatar da cikakken uzuri ga Olajengbesi ta kafafen yada labarai na kasa da kuma shafukan sada zumunta.
Lauyan ya ce idan Fadahunsi bai cika wadannan bukatu cikin sa’o’i 24 ba, zai garzaya kotu domin neman diyyar Naira biliyan 10.
A cewar lauyan, kudin da za a nema zai kasance diyya ta gaba daya da ta musamman kan zargin bata suna da yada bayanan karya masu cutarwa.
Yan sanda sun gayyaci sanatan APC
An ji cewa ’yan sandan Osun sun gayyaci Sanata Francis Fadahunsi, mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, domin ya yi bayani kan kalamansa da suka yadu a kafafen sada zumunta.
Sanatan ya bukaci magoya bayan APC su “kashe” ’yan jam’iyyar Accord idan suka gan su yayin zaben gwamna da za a gudanar a wasu sassan jihar.
Tawagar Fadahunsi ta ce kalamansa ba wai kiran tashin hankali ba ne, illa kira ne ga masu kada kuri’a su yi watsi da Accord ta hanyar amfani da kuri’u.
Asali: Legit.ng