Sanata Lamido Ya Hakura, Ya Fasa Komawa Majalisa saboda Wata Matsala da Ya Gano

Sanata Lamido Ya Hakura, Ya Fasa Komawa Majalisa saboda Wata Matsala da Ya Gano

  • Sanata Ibrahim Lamido ya ce rashin ikon gudanarwa ne ya sa ya hakura da sake neman kujerar sanata na mazabar Sokoto ta Gabas a 2027
  • 'Dan majalisar ya bayyana cewa matsalar tsaro a Sokoto ta Gabas na bukatar shugaba mai ikon aiwatar da tsare-tsaren gwamnati kai tsaye
  • Yayin da ya gaza samun tikitin takarar gwamna a karkashin ADC, Sanata Lamido ya bayyana matakin da ya dauka game da jam'iyyar a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sokoto - Sanata mai wakiltar mazabar Sokoto ta Gabas a majalisar dattawa, Ibrahim Lamido, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai sake neman komawa majalisar tarayya ba a babban zaben shekarar 2027.

Lamido ya ce kujerar sanata ba ta da isasshen ikon gudanarwa da zai ba shi damar tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi yankinsa yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a wurin taro, matasa sun yi kan dan majalisar tarayya, Hon. Sadiq Tafida

Sanata Ibrahim Lamido ya yi magana game da dalilin da ya sanya ba zai sake neman takarar majalisar dattawa ba.
Sanata Ibrahim Lamido zaune a kujerarsa a zauren majalisar dattawa, Abuja. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Dalilin sanatan Sokoto na fasa komawa majalisa

Da yake hira da 'yan jarida a karshen mako, sanatan ya ce bayan ya hakura da komawa zauren majalisar tarayya, ya nemi tikitin takarar gwamnan jihar Sokoto, in ji rahoton Daily Trust.

A cewar Sanata Ibrahim Lamido, ya nemi tikitin takarar a jam'iyyar ADC ne domin ya samu damar magance matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a yankin Sokoto ta Gabas.

A cewar Lamido, al’ummar mazabarsa sun dade suna bukatar ya nemi mukamin gwamna saboda sun yi imanin cewa gwamna ne kadai ke da cikakken iko da kayan aikin da za su taimaka wajen yakar matsalolin tsaro.

Dan majalisar dattawan ya ce:

“Na nemi kujerar gwamna ne saboda matsalar tsaro da ke addabar mutanena. A matsayina na sanata, ba ni da ikon zartarwa wanda ake bukata domin magance wannan matsala yadda ya kamata.”

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa a Najeriya kan yadda shugabanni za su iya taka rawar gani wajen dakile matsalar tsaro, musamman a arewacin kasar nan da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da rikice-rikicen al’umma.

Kara karanta wannan

APC ta hana 'yan siyasa 47 shiga takarar sanata, ta saki cikakken jerin sunayen

Sanata Lamido ya fadi tikitin gwamna a ADC

Sai dai, jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Sanata Ibrahim Lamido bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin jam’iyyar ADC ba.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Mannir Dan’iya, shi ne ya samu tikitin bayan jam’iyyar ta zabi tsarin sulhu wajen fitar da dan takara.

Duk da hakan, Lamido ya bayyana cewa zai ci gaba da biyayya ga jam’iyyar ADC tare da yin aiki domin ganin ta samu nasara a zaben shekarar 2027.

Sanata Ibrahim Lamido ya gaza samun tikitin taarar gwamnan Sokoto a ADC.
Taswirar jihar Sokoto da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lamido ya yi alkawarin mara wa ADC baya

Sanatan ya ce siyasa a wajensa ba ta shafi anfani na kashin kai kawai ba, illa wata hanya ta hidimtawa jama’a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa:

“Zan ci gaba da zama a ADC kuma zan mara wa wanda ya samu tikiti baya. A wajena siyasa ba batun anfani na kai ba ne, hidimtawa jama’a ne.”

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin furucin Sanata Ibrahim Lamido ya nuna yadda wasu ‘yan majalisa ke nuna damuwa kan karancin ikon da suke da shi wajen magance matsalolin tsaro a yankunansu.

Kara karanta wannan

Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau ya janye daga neman takarar dan majalisar wakilai

Rigimar Sanata Lamido da Wammako

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani rikicin cikin gida a APC ya ƙara kamari tsakanin magoya bayan Sanata Ibrahim Lamido da tsohon gwamna Sanata Aliyu Wamakko.

A baya bayan nan ne Sanata Aliyu Wamakko da Shugaban tsagin APC a jihar, Isa Sadiq Achida su ka bayyana shakku a kan asali da ingancin siyasar Ibrahim Lamido.

Isa Sadiq Achida, ya ce ba za a bar Sanata Ibrahim Lamido ya tsaya takara a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ba saboda wadannan zarge-zarge, lamarin ya kuwa ya tabbata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com