Sabuwar Wakar da Rarara Ya Fitar Kan Isa Pantami Ta Tayar da Kura a Arewa
- Fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fitar da sabuwar wakar siyasa da ta shafi Farfesa Isa Ali Pantami, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a Arewa
- A cikin wakar, Rarara ya yi kalaman da suka fusata wasu, inda masu suka suka ce bai dace a ci mutuncin Pantami ba saboda matsayinsa
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya ce adawa da Pantami ya kamata ta kasance bisa hujjoji da bambancin siyasa, ba cin mutunci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Fitaccen mawakin siyasa a Arewacin Najeriya ya sake tayar da kura a yankin bayan fitar da wata sabuwar waka da ta shafi siyasa.
Rarara ya yi wakar ce inda ya ce taba Farfesa Isa Ali Pantami wanda ke neman takarar gwamna a Gombe karkashin jam'iyyar PDP.

Source: Facebook
Mawakin ya fitar da bidiyon wakar ce a shafinsa na Facebook wanda ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mutanen Arewacin Najeriya.
Wakar da Rarara ya sake kan Pantami
Bidiyon wakar ya tayar da magana ne bayan mawakin na kiran Isa Pantami da dan kwaya inda wasu ke cewa bai dace ba ko kadan ya yi wannan kalamai.
Suna ganin cewa a matsayin Pantami na malamin addinin Musulunci, bai kamata ya ci mutuncinsa saboda shi ma almajiri ne a makarantar allo.
Sai dai duk da wasu yan APC sun nuna rashin jin dadi, amma da yawan yan jam'iyyar masu goyon bayanta sun yi farin ciki tare da taya mawaki Rarara yada wakar a shafukansu.
Sashen sharhi na mawakin ya dauki hankali yayin da a wannan lokaci da muke buga wannan rahoton an samu wadanda suka yi sharhi fiye da mutane 13,000.
Har ila yau, fiye da mutane 8,000 ne suka yada rubutu da kuma bidiyon wakar da fitaccen mawakin ya wallafa da ake ta maganganu kan halarcinta a siyasance.

Source: Twitter
Abin da dan APC ya ce kan wakar
Jigon APC a Kano, Bashir Ahmad shi ma ya bayyana fahimtarsa game da wakar da mawakin ya fitar a shafinsa na Facebook.
Tsohon hadimin shugaban kasa ya rubuta cewa:
"Ko da akwai siyasa, amma akwai mutane da darajarsu ta wuce a rika ci musu mutunci saboda irin gagarumar gudunmawar da suka bayarwa ga al’umma.
"Abin da ke ba ni mamaki shi ne, ban san dalilin da ya sa masu adawa da Sheikh Pantami suke fi mayar da hankali wajen cin mutuncinsa, maimakon su yi masa adawa ta hanyar hujjoji, ra’ayi da bambancin siyasa."
Rarara zai shiga yankin Arewa tallata Tinubu
A wani labarin, an ji cewa wasu mambobin tafiyar Triple R sun yi bankwana da kungiyar bayan rikicin da ya taso kan rabon kudi da aka karbo daga 'yan siyasa.
Rahoto ya nuna cewa sakataren kungiyar, Ahmed Bifa ya amince an karbi kudi amma ya musanta cewa kudin ne ya fi muhimmanci a tafiyar.
Bifa ya bayyana cewa tsohon gwamnan Zamfara ya ba tafiyar kudi har Naira miliyan 500 domin tallata shugaban kasa Bola Tinubu a 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng

