Kano Ta Dauki Zafi, Sukar da Kwankwaso Ya Yi wa Malamin Musulunci Ta Harzuka Matasa

Kano Ta Dauki Zafi, Sukar da Kwankwaso Ya Yi wa Malamin Musulunci Ta Harzuka Matasa

  • Wasu matasan Arewa sun soki Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan kalamansa game da matsayar Sheikh Sani Yahaya Jingir
  • Kungiyar ta ce abin da Kwankwaso ya fada kan tikitin Musulmi da Musulmi, ra’ayinsa ne na kansa, ba ra’ayin al’ummar Kano ba
  • Ta sake bayyana goyon bayanta ga tikitin Tinubu da Shettima na Musulmi da Musulmi a babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kungiyar matasan Arewa mi suna, Arewa Youth Merger Group, APC ta soki dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kungiyar matasan ya caccaki Kwankwaso ne kan ikirarinsa cewa al’ummar Kano ba sa goyon bayan kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir game da tikitin shugaban kasa na Musulmi da Musulmi.

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

The Nation ta ruwaito vewa matsayar kungiyar na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugabanta na kasa, Kwamared Musa Mujahid Zaitawa, ya sanya wa hannu tare da rabawa manema labarai.

Kara karanta wannan

Dan Kwankwasiyya da ya rantse da Kur'ani saboda soyayyar Kwankwaso ya koma APC

Kungiyar ta ce sukar da Kwankwaso ya yi wa kalaman Sheikh Jingir ra’ayinsa ne na kansa, ba wai matsayar al’ummar Jihar Kano ba.

Ta kare matsayin Sheikh Jingir

Kungiyar ta ce bai dace Kwankwaso ya tsoma baki cikin ra’ayin malamin addini ba, domin tana ganin yana amfani da hakkinsa na kundin tsarin mulki na bayyana ra’ayinsa a matsayinsa na dan Najeriya.

Sanarwar ta ce:

“Ba daidai ba ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tsoma baki cikin ra’ayin malamin addini wanda yake amfani da hakkinsa na kundin tsarin mulki a matsayinsa na dan Najeriya.”

Ta soki Kwankwaso kan tikitin Musulmi

Kungiyar ta kuma soki Kwankwaso kan adawarsa da tikitin Musulmi da Musulmi, inda ta yi nuni da kalaman Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) kuma tsohon Gwamnan Rivers, Nyesom Wike.

A cewar kungiyar, Wike ya taba bayyana a fili cewa tikitin Musulmi da Musulmi bai saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya maida hankali kan samar da ayyuka masu gwaɓi ga matasan Najeriya

Kungiyar ta kuma yi nuni da matsayin Peter Obi, wanda ta bayyana a matsayin abokin takarar Kwankwaso, tana mai cewa tsohon Gwamnan Anambra ya amince cewa babu matsalar kundin tsarin mulki da tikitin Musulmi da Musulmi.

Ta kuma yi ikirarin cewa Obi ya nemi afuwa kan yadda ya bullo da batun rabuwar addini a yakin neman zabensa na baya.

Sheikh Jingir.
Shugaban Majalisar malamai na kungiyar Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: Abubakar Usman Abubakar
Source: Facebook

Ta ce kalaman Kwankwaso abin kunya ne

Musa Zaitawa ya bayyana sukar da Kwankwaso ya yi wa Sheikh Jingir a matsayin “abin kunya”, tare da kira gare shi da ya guji kalaman da za su iya kara raba kan ‘yan Najeriya saboda dalilan siyasa.

A karshe, kungiyar ta sake tabbatar da goyon bayanta ga tikitin Tinubu da Shettima na Musulmi da Musulmi a babban zaben 2027.

Kwankwaso ya ja hankalin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya kare dimokuraɗiyya, tare da bai wa jam’iyyun adawa dama.

Kwankwaso ya kuma roƙi shugaban ƙasar da ya bai wa jam’iyyun adawa damar gudanar da ayyukansu cikin ’yanci ba tare da tsangwama ba.

Kwankwaso ya ce Tinubu, wanda ya taɓa kasancewa ɗan adawa kafin ya zama shugaban ƙasa, ya kamata ya bar kyakkyawar tarihi ta hanyar kare dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262