An Yi Babbar Asara da Aka Yi Kazamar Arangama tsakanin Matasa da Fulani Makiyaya
- Mutane uku sun jikkata yayin da wani rikicin ya barke tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Kataeregi da ke jihar Neja a Arewacin Najeriya
- Rikicin ya samo asali ne daga takaddamar gonaki da iyakokin filayen noma, lamarin da ya rikida ya zama fada a tsakanin al'ummomin biyu
- Rundunar ’Yan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa an lalata babura hudu yayin rikicin kafin a shawo kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Akalla mutane uku sun jikkata a wani rikici da ya auku tsakanin manoma da makiyaya a yankin Kataeregi da ke karamar hukumar Katcha a jihar Neja.
Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kwantar da tarzomar tare da tabbatar da tsaro a yankin.

Kara karanta wannan
Rigima ta ɓarke tsakanin matasan gari da fulani makiyaya, mutum 3 sun baƙunci lahira

Source: Original
Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddama kan gonaki tsakanin wasu al’ummomin manoma da wani matsuguni makiyaya da ke yankin.
Jami'in hulda da jama'a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar.
Kakakin yan sandan ya bayyana sunayen wadanda suka jikkata da suka hada da Tukur Liti, Ali Liti da Alhaji Ibrahim.
Matasa sun kai hari kan makiyaya
A cewar Abiodun, wasu matasa daga al’ummomin Emitsowa, Emiyagi, Emiworo, Emisheshi da Kakanpangi ne dsuka kai hari kan wani matsugunin makiyaya da ke Kakanpangi.
Ya ce matasan sun kai harin ne kan zargin aikata masu ba daidai ba a gonakindu da kuma takaddamar iyakar gonaki.
SP Abiodun ya ce wani mutum mai suna Moh’d Yamiyagi ne ya jagoranci matasan, suka kai farmaki rugar da makiyayan ke zaune.
Mai magana da yawun yan sandan ya kara da cewa an lalata babura hudu a yayin rikicin.
’Yan sanda sun dawo da zaman lafiya
Kakakin ’yan sandan ya ce jami’an caji ofis na ’yan sanda da ke kauyrn Kataeregi sun gaggauta zuwa wurin bayan samun rahoton rikicin.
Ya ce jami’an sun kwashe mutanen da suka jikkata zuwa asibiti domin a ba su kulawar da ta dace. A cewarsa, shiga tsakanin ’yan sandan ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin.

Source: Twitter
Ana ci gaba da bincike
Abiodun ya ce har yanzu ana ci gaba da binciken lamarin a sashen ’yan sanda na Kataeregi, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba da aka samu yayin da binciken ke gudana.
An kashe mutum 3 a rikicin makiyaya
A wani labarin, kun ji cewa mutane uku sun mutu sakamakon arangama tsakanin fulani makiyaya da matasan kauyen Mwaghavul da ke Mangu a jihar Filato.
Bayan rasa rayukan mutum uku a rikicin, bayanai sun nuna wani mutum daya daga cikin al’ummar garin ya samu raunuka.
Sojoji sun shiga tsakani tare da gudanar da samame da amfani da jiragen sama marasa matuki domin tabbatar da tsaro.
Asali: Legit.ng
