Ministan Tinubu Alkali Ya Bi Sahun Pantami, Ya Janye daga Takarar Gwamna a Gombe

Ministan Tinubu Alkali Ya Bi Sahun Pantami, Ya Janye daga Takarar Gwamna a Gombe

  • Tsohon Ministan Sufurin Najeriya, Sanata Sa’id Ahmed Alƙali, ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a jam'iyya mai mulki ta APC
  • Ya janye ne a lokacin da wani tsohon ministan, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya sanar da janye wa daga takarar, inda ya bayyana dalilansa
  • Sa’id Ahmed Alƙali ya buƙaci shugabannin jam'iyyar APC na ƙasa su soke wasu zaɓukan da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu domin tabbatar da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe - Tsohon Ministan Sufuri kuma ɗaya daga cikin masu neman tikitin gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar APC, Sa’id Ahmed Alƙali, ya sanar da ficewarsa daga zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar za ta gudanar ranar Alhamis.

Janyewar Alƙali na zuwa ne bayan irin matakin da tsohon ministan sadarwa, Farfsa Isa Ali Pantami, ya ɗauka a baya, lamarin da ya ƙara girgiza siyasar APC a jihar.

Kara karanta wannan

Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River

Tsohon minista ya hakura da neman takara a Gombe
Sanata Sa'idu Ahmed Alkali da ya hakura da neman takara a Gombe Hoto: Sen. Sa'idu Ahmed Alkali
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta kawo labarin cewa manyan jagororin APC a Gombe sun nuna goyon baya ga Jamil Isiyaku a matsayin wanda suke so ya zama ɗan takarar jam’iyyar.

Tsohon minista ya hakura da takara a Gombe

Daily Trust ta ruwaito cewa Umar Alkali Jibrin, hadimin tsohon Ministan ne ya tabbatar da janyewar, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda yadda aka gudanar da wasu zaɓukan fitar da gwani da son rai.

Ya bayyana cewa duk da ya bi dukkannin matakan da jam’iyyar ta gindaya domin neman takarar gwamna, daga ciki har da sayen fam da kuma tantancewa, abubuwan da suka faru a zaɓukan fitar da gwanin suka sa ya janye.

A cewarsa, zaɓukan da aka gudanar a mazaɓun Gombe/Kwami/Funakaye da Billiri/Balanga, da kuma yankin Sanatan Gombe ta Tsakiya, sun kasance cike da maguɗi da tauye haƙƙin ’yan takara da magoya bayan jam’iyya.

An nemi shugabannin APC su duba zaben fitar da gwani a Gombe
Shugaban APC na kasa, Farfesa Yilwatda Nentawe Hoto: Prof Yilwatda Nentawe
Source: Facebook

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya

“Sakamakon da aka bayyana a yankunan da abin ya shafa an ƙirƙire su ne kawai domin babu wani sahihin zaɓe da aka gudanar cikin gaskiya da adalci.”

An zargi jam'iyyar APC da magudi

Alƙali ya kuma yi zargin cewa masu shirya zaɓukan sun karya dokar zaɓe da kuma ƙa’idojin APC da suka tanadi yadda ake gudanar da zaɓukan fitar da gwani kai tsaye.

Ya ce an gudanar da zaɓukan ba tare da wadatattun kayan aiki, jami’an zaɓe, masu sa ido da sauran abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da sahihin tsarin dimokuraɗiyya ba.

Tsohon ministan ya ce irin waɗannan matsaloli sun sa mutane da dama sun rasa amincewa da tsarin zaɓen jam’iyyar. A cewarsa, ba zai shiga abin da ya kira tsarin da aka riga aka murɗe ba.

Duk da janyewarsa daga takarar gwamna, Alƙali ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a APC kuma zai ci gaba da yi wa jam’iyyar aiki domin samun nasara a zaɓen 2027.

Haka kuma ya yi kira ga shugabannin APC na ƙasa su soke zaɓukan da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu tare da kafa sabon kwamitin da zai gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a Kaduna, zaben fitar da gwani ya jefa shugaban APC a matsala

Gombe: Tsohon minista ya janye takara

A baya, mun kawo labarin cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya janye daga zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Gombe da APC ta shirya gudanarwa saboda wasu zarge zarge da ake yi masu.

Tsohon ministan ya bayyana cewa ba a bai wa masu neman takara bayanan da suka dace kan wurin zabe da yadda za a tantance wakilai ba, wanda ke nufin an yi magudi a lamarin.

Farfesa Pantami wanda fitaccen malamin addinin musulunci ne ya ce dama ya shiga neman takarar gwamnan ne bayan kiraye kirayen al'umma, amma yanzu ba zai iya ba saboda matsalolin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng