Tura Ta kai Bango: Amurka za Ta Dauki Matakin da ba a Taba Dauka ba a kan Iran

Tura Ta kai Bango: Amurka za Ta Dauki Matakin da ba a Taba Dauka ba a kan Iran

  • Rahoto ya nuna cewa Ministan Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce Washington za ta ɗauki wasu matakai masu tsauri kan Iran
  • Bessent ya ce matakan za su haɗa da killace tattalin arzikin Iran da kuma ci gaba da katange mashigar ruwan Hormuz
  • Ya bayyana hakan ne yayin da tattaunawar Amurka da Iran kan kawo ƙarshen rikicin da sake buɗe mashigar Hormuz ke fuskantar tsaiko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Ministan Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce gwamnatin Donald Trump za ta ɗauki matakan da ba a taɓa ganin irinsu ba kan Iran.

Bessent ya ce Washington na shirin ƙara matsin tattalin arziki kan Tehran yayin da rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da tsananta.

Shugaba Donald Trump a Amurka
Lokacin da Donald Trup ke sauraron wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka za ta kuntatawa Iran

Kara karanta wannan

Amurka ta nuna ba daga kafa, ta caccaki Isra'ila kan taba kawayen Iran a Lebanon

Reuters ta wallafa cewa Bessent ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman game da lamuran yau da kullum a kasar Amurka.

Ya ce Amurka za ta sanar da wasu sababbin matakai a mako mai zuwa, yana mai cewa za su kasance cikin matakan killace tattalin arzikin ƙasa mafi tsauri da duniya ta taɓa gani.

“Ku jira wasu sanarwa da za su zo mako mai zuwa, saboda za mu ɗauki matakan da ba a taɓa ganin irinsu ba a tarihin killace tattalin arzikin wata ƙasa,”

In ji shi.

Za a ci gaba da katange Hormuz

Anadolu ta wallafa cewa Bessent ya ce sabbin matakan za su haɗa da killace tattalin arzikin Iran da kuma ci gaba da toshe hanyoyin shiga da fita daga tashoshin jiragen ruwa na ƙasar.

Ya ce hakan zai shafi mashigar ruwan Hormuz, wadda ke da muhimmiyar rawa wajen safarar man fetur da iskar gas a duniya.

“Za a haɗa killace tattalin arziki irin wanda duniya ba ta taɓa gani ba da kuma ci gaba da katange mashigar Hormuz,” in ji Bessent."

Kara karanta wannan

Trump ya sake cika baki kan mashigar Homruz da ake takaddama a kai da Iran

Matakin na zuwa ne bayan Amurka da Iran sun kasa cimma yarjejeniya kan kawo ƙarshen rikicin da ya shafi ƙasashen biyu.

A yanzu haka dai duniya ta zuba ido domin ganin irin matakin da Amurka za ta dauka da yadda zai iya tasiri kan Iran ko akasin haka.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ba ta yi martani ba

Ya zuwa yanzu, Iran ba ta mayar da wani cikakken martani kan barazanar da Bessent ya yi na ƙara matsin tattalin arziki ba.

Sai dai rikicin ya riga ya shafi zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, inda adadin jiragen da ke wucewa ya ragu matuka idan aka kwatanta da lokacin kafin rikicin.

Iran ta gargadi kasar Faransa

A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi wa kasar Faransa martanin kan sukar da ta masu game da hukuncin kisa.

Ministan ya bayyana cewa Faransa ba ta da hurumin tsoma baki a harkokin wasu ƙasashe lura da cewa tana goyon bayan kisan da Isra'ila ke yi.

Haka zalika Idan ta caccaki kasashen Turai da suka tsoma baki kan wasu matakai da ta dauka game da tsaron ta a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng