Gwamna Dikko Radda Ya Samu Tikitin APC, Zai Nemi Tazarce a Zaben Gwamnoni na 2027
- Jam'iyyar APC ta tabbatar da Malam Dikko Radda a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Katsina a babban zaben 2027
- Gwamna Dikko Radda ya samu tikitin tazarce karo na biyu ba tare da hamayya ba a taron da aka gudanar yau Alhamis a birnin Katsina
- Malam Dikko, wanda zai nemi wa'adi na biyu a 2027, ya gode wa wakilan APC da al'ummar jihar bisa amincewar da suka nuna masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Gwamna Dikko Radda ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Katsina domin neman tazarce a zaɓen 2027.
Wakilan jam’iyyar APC ne suka tabbatar da Gwamna Dikko Radda a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2027 ta hanyar maslaha a ranar Alhamis.

Source: Facebook
Channels tv ta rahoto cewa an gudanar da taron tabbatarwar ne a Katsina People’s Square, inda jimillar wakilai 2,835 suka amince da takarar Radda karo na biyu.
Yadda aka tabbatar da Dikko Radda
Da yake gabatar da gwamnan ga magoya bayan APC, shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani, Yakubu Machido, ya bayyana Radda a matsayin ɗan takarar APC ta hanyar maslaha.
Ya ce babu wanda ya fito neman takarar gwamnan Katsina a inuwar APC, don haka aka tabbatar da Malam Dikko Radda ba tare da hamayya ba.
APC ta yaba da haɗin kai mambobinta
A jawabinsa, mataimakin shugaban APC na ƙasa mai kula da yankin Arewa maso Yamma, Muhammad Garba, ya ce aikin kwamitin shi ne tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin lumana da sahihanci.
A cewarsa, nasarar taron ta samu ne saboda ƙoƙarin Gwamna Radda da kuma haɗin kan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a faɗin jihar.
Masari ya yi kira ga haɗin kai
Tsohon gwamnan jihar Katsina kuma shugaban kwamitin sulhu na APC, Aminu Masari, ya yabawa mambobin jam’iyyar saboda kiyaye zaman lafiya yayin gudanar da taron.

Kara karanta wannan
Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye
"Dole mu hada kai mu maida hankalin mu kacokan wajen tabbatar da nasarar dukkan ‘yan takarar APC,” in ji shi.

Source: Facebook
Dikko Radda ya gode wa magoya baya
A jawabin karɓar takara, Gwamna Radda ya gode wa wakilai, shugabannin jam’iyya da magoya baya bisa amincewar da suka nuna masa, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Ya tabbatar wa al’ummar Katsina cewa ba zai ba su kunya ba, sannan ya yi kira da a ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar APC baya a zaɓe mai zuwa.
An kammala taron ne da miƙa tutar APC ga Gwamna Radda daga hannun mataimakin shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa maso Yamma, wanda hakan ya tabbatar da shi a hukumance a matsayin ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen 2027.
Gwamna Fubara ya janye takara a APC
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya hakura da neman tazarce karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2027.
Fubara ya ce bayan dogon tunani da tattaunawa da iyalansa, abokai da makusantansa, ya yanke shawarar janyewa daga neman takara.
Gwamna Fubara ya tabbatar da cewa yana nan daram a APC, kuma zai mara wa duk wanda ya samu tikitin jam’iyyar baya a zaben 2027.
Asali: Legit.ng
