ICPC ta Bankado Jami’in da Ya Dora Iyalansa 14 kan Tsarin Albashin Gwamnati

ICPC ta Bankado Jami’in da Ya Dora Iyalansa 14 kan Tsarin Albashin Gwamnati

  • Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gano wani jami’in gwamnati da ya saka mutum 14 daga cikin iyalansa a cikin jerin ma’aikatan gwamnati
  • An kuma gano wani mutum da ya yi wa matarsa, ’ya’yansa da wasu ’yan uwansa rajista, inda suke karɓar albashi 13 a kowane watan duniya
  • Hukumar ICPC ta ce ta gano kusan ma’aikatan bogi 900, tare da kwato sama da N24bn na kudin fanshon bogi a shekarar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja– Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta gano wasu hanyoyin da ake amfani da su wajen damfarar albashin gwamnati.

Daga cikin abubuwan da aka gano akwai wani jami’in da ya saka mutum 14 daga cikin iyalansa cikin jerin ma’aikatan gwamnati.

Kara karanta wannan

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Jariri sabon haihuwa da aka sace ya kubuta

ICPC ta yi bincike kan ma'aikatan bogi
Ginin hukumar yaki da rashawa ta ICPC Hoto: ICPC
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa hukumar ta kuma gano wani mutum da ake zargi da saka matarsa, ’ya’yansa da wasu ’yan uwansa cikin tsarin albashin gwamnati, inda suka rika karɓar albashi har guda 13.

ICPC ta yi bankada

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa shugaban ICPC, Musa Aliyu, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis 13 ga watan Agusta, 2026.

Musa Aliyu ya ce binciken da hukumar ta gudanar kan ma’aikatan bogi ya bankado yadda wasu mutane ke amfani da gibi a tsarin biyan albashin gwamnati wajen karɓar albashi fiye da ɗaya.

“Mun gano mutum guda da ya saka mutum 14 daga cikin iyalansa."

Shugaban ICPC ya ce hukumar ta gano kusan ma’aikatan bogi 900 tare da wallafa sunayensu, tana ƙalubalantar mutanen da abin ya shafa da su tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati ne na gaske.

ICPC an gano ma'aikatan bogi

Shugaban ya ce hukumar ta shafe kusan shekara guda tana gudanar da bincike kan ma’aikatan bogin da ake zargi da su, tare da gano yadda ake saka sunayen ƙarya cikin tsarin biyan albashin gwamnati.

Kara karanta wannan

Hukumar alhazai ta sanar da kuɗin kujerar hajjin shekarar 2027 a jihar Kano

Ana zargin ma'aikatan sun yi wa iyalansu hanya ana ba su albashi
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya ce:

“Wani lokaci idan suka saka sunayensu, za ka ga sunan a cikin tsarin albashi. Za ka ga imel ɗinsu. Amma idan ka duba lambar asusun banki, za ka ga sunan wani mutum. Haka ake yin waɗannan abubuwan."

Aliyu ya yi gargadin cewa matsalar ma’aikatan bogi ba ta tsaya kan albashi kawai ba, domin tana iya haifar da wasu damfarar alawus da fa’idodin gwamnati kamar fansho, jinginar gidaje, tallafin gidaje da inshorar lafiya.

Shugaban hukumar ya ce ICPC na ƙara mayar da hankali kan dakile cin hanci da rashawa da kuma kare dukiyar gwamnati ta hanyar shiga tsakani, maimakon dogaro kawai da gurfanar da mutane a gaban kotu.

ICPC ta gana da Gbajabiamila

A baya, mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci ta yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta titsiye Femi Gbajabiamila kan zargin da ake yi game da PFIPC da ake takaddama a kai.

Kara karanta wannan

ADC ta ji kamshin hadakar 'yan adawa, ana son tsayar da dan takara 1 ya tunkari Tinubu

Mai ikirarin shugabantar PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya zargi Femi Gbajabiamila da karɓar Naira miliyan 400 domin ya samu shugabancin hukumar da aka tabbatar da cewa haramtacciya ce.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar ya musanta zarge-zargen tare da shigar da ƙarar N15bn kan Adeniyi inda a gefe guda ita ma gwamnatin tarayya ta mara masa baya game da zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng