"Neman Tutar APC aka Daina": 'Dan Pantami Ya Ce Takarar Gwamnan Gombe na nan

"Neman Tutar APC aka Daina": 'Dan Pantami Ya Ce Takarar Gwamnan Gombe na nan

  • AbdulRahman Isa Pantami, 'dan tsohon ministan a Najeriya, ya yi gyara a rahotannin da ke cewa mahaifinsa, Isa Ali Pantami ya hakura da neman takara
  • A ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026 ne aka samu rahotannin da suka ce Farfesa Ali Pantami ya hakura da batun neman takarar gwamna a Gombe
  • A karin bayanin da ya fitar, AbdulRahman Isa Pantami ya yi karin haske game da batun, inda ya bayyana cewa maganar neman takarar gwamna na nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – AbdulRahman Isa Pantami, 'dan tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa mahaifinsa bai janye daga neman takarar gwamnan Jihar Gombe ba.

Wannan ya biyo bayan rahotanni da ke cewa Farfesa Isa Pantami ya hakura da batun neman takarar gwamna a bayan zarge-zargen rashin adalci a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Pantami ya fusata, ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a APC, ya fadi dalili

Yaron Pantami ta ce mahaifinsa zai nemi takara a Gombe
Farfesa Isa Ali Pantami tare da magoya bayansa Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da AbdulRahman ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, ya bayyana cewa ba wai Farfesa Isa Pantami ya hakura da maganar neman takara gaba daya ba ne.

AbdulRahman ya magantu game da takarar Pantami

A cikin sanarwar AbdulRahman Isa Pantami, an ce labarin da aka wallafa cewa Pantami ya janye daga neman takarar ba gaskiya ba ne.

Ya yi gyara da cewa sanarwar mahaifinsa ya hakura da neman takara a karkashin jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Gombe.

Sheikh Pantami zai nemi takara, za a fitar da bayanai nan gaba
Farfesa Isa Ali Pantami a wurin karatu a masallacinsa da ke Abuja Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A kalamansa

“An kawo mana rahotannin da ke cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya janye daga takarar gwamnan Jihar Gombe, wannan labari ba gaskiya ba ne."

Ta kara da cewa Pantami yana nan daram a tafiyarsa ta siyasa kuma bai sauya matsayi ba, duk da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu tashoshin labarai.

Pantamiyya za ta sanar da matakai na gaba

Kara karanta wannan

"Na kira shugaban APC," Murray Bruce ya yi fatali da rahoton hana shi takarar sanata

Sanarwar ta kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba, kungiyar Pantamiyya za ta sanar da mabiyanta, magoya baya da masoya Farfesa Isa Ali Pantami a jihar Gombe da ma sauran sassan Najeriya matakan da za su dauka na gaba.

A cewar sanarwar, manufar kungiyar ita ce tabbatar da shugabanci na gari a Gombe da Najeriya gaba daya, tare da tsayawa kan akidar bin doka da oda wajen tunkarar duk wani kalubale na siyasa.

A kalamansa:

"Nan ba da dadewa ba tafiyar Pantamiyya za ta sanar da mabiyanta, magoya baya, masu fatan alheri ga maigidanmu Farfesa Isa Ali Pantami a jihar Gombe da fadin Najeriya mayakan da za ta dauka a nan gaba."

Pantami ya fusata da neman takara a Gombe

A baya, mun kawo labarin cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya janye daga zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Gombe da APC ta shirya gudanarwa saboda wasu zarge zarge na rashin adalci.

Tsohon ministan wanda ya yi aiki a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba a bai wa masu neman takara bayanan da suka dace kan wurin zabe da yadda za a tantance wakilai ba.

Pantami, wanda fitaccen malamin addinin Musulunci ne ya ce dama ya shiga neman takarar gwamnan ne bayan kiraye kirayen al'umma, amma yanzu ba zai iya ba saboda matsaloli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng