Amurka Ta Nuna ba Daga Kafa, Ta Caccaki Isra'ila kan Taba Kawayen Iran a Lebanon
- Gwamnatin Donald Trump ta soki Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, bayan ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa a kudancin Lebanon
- Amurka ta ce zaman sojojin Isra’ila na dindindin a kudancin Lebanon ya saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma da kuma alkawarin mutunta Lebanon
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta jaddada goyon bayanta ga cikakken ikon mallakar Lebanon da kuma kare mutuncin iyakokinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Gwamnatin Amurka ta soki kalaman Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, bayan ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa a yankunan tsaro da ke kudancin Lebanon.
Katz ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai kudancin Lebanon, inda ya ce Isra’ila ba za ta janye sojojinta daga yankunan da ta kira na tsaro ba.

Source: Getty Images
Amurka ta accaki Isra'ila
Arab News ta wallafa cewa wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce Washington na sa ran dukkan ɓangarorin da abin ya shafa za su mutunta tsarin da suka amince da shi kan Lebanon.
Jami’in ya ce Isra’ila ta bayyana a fili cewa ba ta da wata manufar mallakar wani yanki na Lebanon kuma ana bukatar ta tabbatar da hakan.
Ya ce kasancewar sojojin Isra’ila na dindindin a kudancin Lebanon bai dace da alkawuran da aka ɗauka ko kuma burin samar da zaman lafiya da tsaro na dogon lokaci tsakanin ƙasashen biyu ba.
Amurka ta goyi bayan Lebanon
Reuter ta wallafa cewa jami’in na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce Amurka tana goyon bayan cikakken ikon mallakar Lebanon da kuma mutuncin yankinta.
Ya ce yarjejeniyar da Washington ta taimaka wajen cimmawa tsakanin Isra’ila da Lebanon ta tanadi tsarin janye sojojin Isra’ila a hankali.
Sai dai ya ce hakan yana da alaƙa da tabbatar da kwance damarar Hezbollah da kuma rusa abubuwan more rayuwarta na soji.

Source: Getty Images
Sojojin Lebanon sun fara aiki
Jami’in ya ce rundunar sojin Lebanon ta fara aiwatar da tsarin a wani yanki a Kudancin ƙasar domin tabbatar da tsaro.
Ya ce Amurka za ta ci gaba da tallafa wa cikakken aiwatar da tsarin da aka tsara domin tabbatar da tsaro da ikon gwamnatin Lebanon a yankin.
Rahoto ya nuna cewa yankin ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da sojojin Isra’ila suka janye, sannan sojojin Lebanon suka maye gurbinsu.
Iran ta zargi kasar Faransa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya soki Faransa da wasu ƙasashe kan abin da ya kira “munafunci” wajen magana kan haƙƙin ɗan Adam da dokokin ƙasa da ƙasa.
Araghchi ya ce ƙasashe irin Faransa ya kamata su daina wa duniya wa’azi kan haƙƙin ɗan Adam da dokokin ƙasa da ƙasa.
Ya zargi Faransa da goyon bayan Isra’ila a yakin Gaza da kuma abin da ya kira ta’addancin Isra’ila kan Iran, yana mai cewa hakan ya lalata duk wata damar da ƙasar ke da ita ta yin ikirarin kula da dan Adam.
Asali: Legit.ng

