Babban Sarki Ya ba da Mamaki, Ya Fadi Gaskiya a Idon Tinubu kan Ta'addanci
- Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan yadda gwamnatinsa ta garkuwa da mutane
- Ladoja ya ce kin biyan kuɗin fansa da gwamnatin tarayya ta yi ya ƙara ƙarfin gwiwar jama'a, tare da neman a ci gaba da tsaron dazukan Oyo
- Tinubu ya ce jami'an tsaro sun ceto ɗalibai da malamai ba tare da biyan kuɗin fansa ba, bayan amfani da bayanan sirri da kama wasu da ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Oyo, Ibadan - Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, ya yi magana game da kokarin Bola Tinubu kan ayyukan ta'addanci.
Basaraken ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda gwamnatinsa ke tunkarar matsalar satar mutane a Najeriya.

Source: Facebook
Ladoja ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya
Yadda Tinubu ya kawo sauyi a bangaren tsaro
Ya ce shugaban ya kawo gagarumin sauyi a yaƙi da garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci.
Ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin tsaro a Oyo.
Ziyarar ta biyo bayan sace ɗalibai da malamai da aka yi kwanan nan a ƙaramar hukumar Oriire.
Taron ya mayar da hankali kan yadda za a hana masu garkuwa da mutane sake samun mafaka.
Hotuna da bidiyon taron da suka bazu sun nuna cewa Alaafin na Oyo, Oba Hakeem Owoade, bai halarci ganawar da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa ba.

Source: UGC
Ƴan bindiga: An yabawa Bola Tinubu
Da yake jawabi a madadin Majalisar Sarakunan Oyo, Ladoja ya yaba wa Tinubu saboda kin amincewa da biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, cewar Daily Post.
Ya ce a lokacin da aka yi garkuwa da mutanen, al'ummar Oyo sun shiga fargaba sosai, amma haɗin gwiwar jami'an tsaro ya sauya yanayin tare da dawo da kwarin gwiwar jama'a.
Ladoja ya kuma shawarci shugaban ƙasa da kada a yi watsi da dazukan da ke iyakar Oyo da Neja, a cewarsa, ci gaba da kasancewar jami'an tsaro a yankin zai hana masu laifi dawowa.
Yabon da sarkin ya yi ya zo ne bayan Tinubu ya bayyana cewa jami'an tsaro sun ceto ɗaliban da malamansu ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Shugaban ya ce gwamnati ta ƙi tattaunawa da masu garkuwa da mutane saboda biyan kuɗin fansa na ƙarfafa masu laifi su ci gaba da aikata irin wannan ta'asa.
Tinubu ya bayyana cewa jami'an tsaro sun yi amfani da sahihan bayanan sirri wajen gano hanyar masu garkuwar, haka kuma sun kama wasu daga cikin iyalansu da masu taimaka musu.
A ƙarshe, masu garkuwar sun saki waɗanda suka sace ba tare da karɓar ko sisi na kuɗin fansa ba. Bayan kwashe kusan kwanaki 56 a tsare, an ceto mutanen tare da kama mutum takwas, yayin da aka kashe wasu.
Gadar sama: Tinubu ya shawarci gwamnoni
An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi su fifita gina hanyoyi maimakon wasu ayyuka da ke cin kudi kuma marasa amfani.
Tinubu ya ce gwamnati ba ta biya kuɗin fansa ga masu satar ɗaliban makarantar Oriire ba, yana mai jaddada cewa babu sasanci.
Shugaban ya bayyana shirin faɗaɗa rundunar soji zuwa rukunoni 12, ƙarfafa masu gadin dazuka da kafa ‘yan sandan jihohi.
Asali: Legit.ng

