Shugabancin Majalisar Dinkin Duniya: An Buƙaci Tinubu Ya Tura Sunan Jonathan
- Ƙungiyar APRC ta ba Shugaban kasa, Bola Tinubu shawara game da shugabancin Majalisar Dinkin Duniya
- Ta bukaci Tinubu ya tsayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan takarar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya
- APRC ta ce Jonathan ya mallaki gogewar shugabanci, ƙwarewar diflomasiyya da tarihin kare dimokuraɗiyya da suka dace da jagorantar Majalisar Ɗinkin Duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban ƙungiyar African Policy and Research Consortium (APRC), Farfesa Edward Agbai, ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Agbai ya bukaci Tinubu ya tsayar da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar Najeriya na mukamin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Source: Getty Images
Ya ce Jonathan ya cancanci wannan matsayi saboda gogewarsa da ƙwarewarsa, cewar Punch.
Cancantar da Jonathan ke da ita

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su
Agbai ya bayyana cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na buƙatar jagora mai gogewar shugabanci, tarihin kare dimokuraɗiyya da kuma ƙwarewar magance manyan ƙalubalen duniya.
Ya ce Jonathan ya cika waɗannan sharuɗɗa saboda irin ayyukan da ya gudanar lokacin yana kan mulki.
Ƙungiyar ta tuna cewa Jonathan ya kasance mataimakin shugaban ƙasa tsakanin shekarun 2007 zuwa 2010, sannan ya zama shugaban ƙasa daga 2010 zuwa 2015.
Ta ce irin yadda ya gudanar da mulki ya nuna yana da ƙwarewa da jajircewa wajen shugabanci nagari.
APRC ta yabawa Jonathan kan yadda ya amince da shan kaye bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2015.
Ta ce wannan mataki ya ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya, ya kuma nuna girmamawarsa ga kundin tsarin mulki da zaman lafiyar ƙasa.

Source: Twitter
Kokarin Jonathan ya bar mulki
Ƙungiyar ta ƙara da cewa bayan barinsa mulki, Jonathan ya ci gaba da tallafa wa dimokuraɗiyya, gina zaman lafiya da sasanta rikice-rikice a sassa daban-daban na Afirka ta hanyar sa ido kan zaɓe da shiga aikin sulhu.
Ta bayyana cewa Jonathan ya gudanar da waɗannan ayyuka ne tare da ƙungiyoyi irin su Tarayyar Afirka, ECOWAS, COMESA, IGAD da kuma West African Elders Forum, lamarin da ya ƙara masa kima a idon ƙasashen duniya.
A cewar APRC, salon Jonathan na tattaunawa, shawarwari da gina matsaya ɗaya ya sa ya samu karɓuwa a duniya, cewar Tribune.
Ta ce waɗannan halaye suna da matuƙar muhimmanci ga duk wanda zai jagoranci Majalisar Ɗinkin Duniya wajen sasanta rikice-rikice da bunƙasa haɗin kan ƙasashe.
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da ƙasashen Afirka da sauran abokan hulɗa na duniya domin neman goyon baya ga takarar Jonathan.
Takarar Obi: Jonathan ya musanta karbar cin hanci
An ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya martani kan rahoton da ke cewa an yi masa tayin Naira biliyan 500 domin ya tsaya takara.
Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai ya ne ya yi martani a madadinsa bayan an fara raɗe-raɗin ya karɓo kwangilar raba ƙuri'ar Peter Obi.
Raɗe-raɗin na kara yin karfi ne bayan rahotanni na ci gaba da cin karo da juna a kan zai tsaya wa tsagin PDP takarar shugaban ƙasa a 2027.
Asali: Legit.ng
