Peter Obi Ya Dura kan Tinubu bayan Ya Yi Kalamai kan Yunwa a Najeriya
- Peter Obi ya ce kalaman Shugaba Bola Tinubu kan yunwa ba su yi la’akari da tsananin wahalar da miliyoyin ’yan Najeriya ke ciki ba
- Ya ce adadin mutanen da ke fuskantar matsanancin rashin abinci ya karu daga kimanin miliyan 17 zuwa miliyan 35 tun bayan hawan gwamnatin Tinubu
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bukaci gwamnati ta zuba jari a fannin ilimi, lafiya, noma, tsaro da kananan sana’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kalamansa na baya-bayan nan game da yunwa a Najeriya.
Obi ya bayyana cewa kalaman shugaban kasar ba su nuna damuwa da tsananin matsin tattalin arziki da miliyoyin ’yan Najeriya ke fuskanta ba.

Source: Facebook
A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 31 ga watan Yulin 2026 a shafinsa na X, Obi ya ce ya damu da kalaman da Tinubu ya yi wa wasu limaman cocin Katolika cewa yunwa ta dade tana akwai a Najeriya tun kafin a haife shi.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi yadda za a hana gwamnoni amfani da 'yan sanda jihohi ba bisa ka'ida ba
Wane martani Peter Obi ya yi wa Tinubu?
Obi ya ce duk da cewa yunwa ta dade tana kasancewa a Najeriya, kalaman shugaban kasar ba su bayyana girman matsalar tattalin arzikin da ’yan kasa ke fuskanta a halin yanzu ba.
“Na kalla cikin matukar damuwa kalaman da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa limaman cocin Katolika da suka ziyarce shi a ofishinsa, cewa yunwa ta dade tana a Najeriya tun kafin a haife shi.”
“Duk da cewa gaskiya ne yunwa ta kasance wani bangare na rayuwar dan Adam kuma ta dade a kasarmu, irin wannan magana na iya zama kamar rashin nuna damuwa da halin da miliyoyin ’yan Najeriya ke ciki sakamakon tsananin matsin tattalin arziki.”
- Peter Obi
Obi ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a mayar da hankali kan bayanai na gaskiya da kuma sakamakon da ake iya aunawa na yadda ake gudanar da mulki.
Matsalar rashin abinci ta karu
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce matsalar rashin wadataccen abinci ta kara ta’azzara tun bayan da gwamnatin Tinubu ta hau mulki a shekarar 2023.
A cewarsa, kimanin ’yan Najeriya miliyan 17 ne ke fuskantar matsanancin rashin abinci kafin gwamnatin mai ci ta karbi mulki.
Obi ya ce adadin ya karu zuwa kusan miliyan 35 a halin yanzu.
“Maimakon a inganta lamarin, matsalar ta kara ta’azzara sosai a karkashin gwamnatin da ke mulki yanzu.”
- Peter Obi
Obi ya yi magana kan talauci
Peter Obi ya kuma yi ikirarin cewa matakin talauci ya karu a lokacin gwamnatin Tinubu.
Ya ce adadin ’yan Najeriya da ke rayuwa cikin matsanancin talauci ya karu daga kimanin miliyan 87 a shekarar 2023 zuwa kusan miliyan 140.
Tsohon gwamnan ya amince cewa gwamnatin Tinubu ta gaji manyan kalubale na tattalin arziki da tsaro.

Source: Facebook
Sai dai ya ce ya kamata a auna nagartar shugabanci ne bisa yadda gwamnati ta inganta rayuwar jama’a.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
“Babu wanda ke musanta cewa wannan gwamnati ta gaji manyan kalubale. Amma ana auna shugabanci ne ba da kalubalen da aka gada ba, sai dai da sakamakon da aka samu.”
“Dole gwamnati ta amince da gaskiya cewa matakan da ta dauka ba su kai yadda yanayin matsalar ya bukata ba, yayin da karin miliyoyin ’yan Najeriya suka kara nutsewa cikin talauci da yunwa.”
- Peter Obi
Peter Obi ya shawarci Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cew dn takarar shugaban ƙasa na jam'iyyae NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya soki salon isar da sakon Shugaba Bola Tinubu.
Peter Obi ya roƙi shugaban kasar da ya riƙa yi wa ’yan Najeriya magana kai tsaye game da halin da ƙasar ke ciki.
Asali: Legit.ng
