Ana Wata ga Wata: Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Nada Hadimi a Bangaren Rawa
- Shugaban ƙaramar hukumar Kuje, Danjuma Shekwolo, ya naɗa wani matashi a matsayin hadiminsa a bangaren rawa
- Takardar naɗin ta ce an ba Danladi mukamin ne saboda jajircewa, ƙwazo da gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ƙaramar hukumar Kuje
- Shekwolo ya ce an samu kuskuren fahimta, yana mai jaddada cewa mukamin da aka ba Danladi shi ne mataimaki na musamman kan harkokin nishaɗi, ba rawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban ƙaramar hukumar Kuje da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, Danjuma Shekwolo, ya ba da mamaki bayan wani nadin hadimi da ya yi.
Shekwolo ya naɗa Ibrahim Danladi a matsayin mataimaki na musamman bangaren rawa domin shakatawa.

Source: Original
Takardar naɗin ta fito ne da kwanan watan 13 ga Yuli kuma ta fara aiki nan take, cewar rahoton TheCable.
Takardar mai lamba KAC/CHM/30/VOL.1 ta bayyana cewa an ba Danladi wannan mukami ne saboda ƙwazo, sadaukarwa, jajircewa da gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa ƙaramar hukumar Kuje.
A cikin takardar, shugaban ya buƙaci sabon mataimakin ya tabbatar da amincewar da aka nuna masa ta hanyar gudanar da ayyukansa cikin gaskiya da ƙwazo domin amfanin al'umma.
Takardar ta bayyana mukamin a matsayin Mataimaki na Musamman kan Rawa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bazu a kafafen yaɗa labarai.

Source: Twitter
Sai dai da yake magana da manema labarai, Shekwolo ya musanta cewa ya naɗa mataimaki kan rawa kawai, yana cewa an yi kuskuren fahimtar abin da mukamin yake nufi.
Ya ce ainihin mukamin da aka ba Danladi shi ne Mataimaki na Musamman kan Harkokin Nishaɗi, ba mataimaki kan rawa ba kamar yadda wasu suka ruwaito.
An tuna cewa Shekwolo, ɗan takarar APC, ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Kuje a watan Fabrairu bayan samun ƙuri'u 17,269, inda ya kayar da Zakwoyi Danlami na PDP wanda ya samu ƙuri'u 15,824.
Shugaban ya bayyana fatansa cewa sabon mataimakin zai cika burin gwamnatin ƙaramar hukumar ta hanyar gudanar da aikinsa yadda ya dace da kuma ba da gudummawa ga ci gaban Kuje.
An tuna cewa Shekwolo, ɗan takarar APC, ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Kuje a watan Fabrairu bayan samun ƙuri'u 17,269, inda ya kayar da Zakwoyi Danlami na PDP wanda ya samu ƙuri'u 15,824.
Shugaban ya bayyana fatansa cewa sabon mataimakin zai cika burin gwamnatin ƙaramar hukumar ta hanyar gudanar da aikinsa yadda ya dace da kuma ba da gudummawa ga ci gaban Kuje.
Ciyaman ya nada hadimai 100 a Rivers
A baya, kun ji cewa shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, Chijioke Ihunwo ya yi abin a yaba kan nadin mukamai da ya yi a ofishinsa.
Ihunwo ya nada akalla masu ba shi shawara na musamman guda 100 da za su taimaka masa a shugabancinsa lamarin da ya jawo maganganu.
Shugaban karamar hukumar ya bukaci sababbin masu mukaman da su tabbatar da yin aiki tukuru a jihar domin samar da shugabanci nagari.
Asali: Legit.ng

