Jihohin Arewa 7 Sun Shirya Yaki domin Tabbatar da Nasarar Tinubu a 2027

Jihohin Arewa 7 Sun Shirya Yaki domin Tabbatar da Nasarar Tinubu a 2027

  • Jam'iyyar APC shiyyar Arewa maso Yamma ta sanar da fara rangadin jihohi bakwai domin ƙarfafa goyon bayan sake zaɓeta
  • Shugabannin jam'iyyar sun ce za su ƙarfafa haɗin kan APC da tattara magoya baya a matakin ƙasa da fatan zarce yawan ƙuri'un fiye da 2023
  • APC ta yabawa Gwamna Uba Sani bisa ba sakatariyar shiyyar mota, tare da jinjinawa gwamnoni da manyan shugabannin yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Jam’iyyar APC ta shiyyar Arewa maso Yamma ta bayyana shirin fara rangadin jihohi bakwai na yankin domin zaben 2027.

APC ta ce ta shirya hakan ne domin ƙarfafa goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ƙarfafa jam’iyyar kafin babban zaɓen shekarar 2027.

APC a Arewa ta shirya neman kuri'u ga Tinubu, Uba Sani
Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Uba Sani.
Source: Twitter

Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na APC a Arewa maso Yamma, Musa Mada, ya fitar ta ce yankin na da muhimmiyar rawa ga jam’iyyar saboda irin yawan ƙuri’un da ya bai wa Tinubu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

NNPP, NDC sun fara zazzafar musayar yawu game da takarar Obi da Kwankwaso

Shirin APC a Arewa maso Yamma

An cimma wannan matsaya ne a taron shugabannin APC na shiyyar da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Kaduna, inda suka duba yanayin siyasa tare da amincewa da ƙara wayar da kan jama'a.

Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Sakataren APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Isah Achida, yayin da Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da shiyyar, Garba Datti, bai halarta ba.

Jam’iyyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa za ta zarce nasarar da ta samu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ta hanyar fara shirye-shirye tun da wuri.

A cewar sanarwar, shugabannin shiyyar sun amince su kai ziyara jihohin Arewa maso Yamma domin tattaunawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin ƙarfafa APC.

APC ta kuma bayyana cewa wannan ne karon farko tun bayan ƙirƙirar jihohi da dukkan jihohin Arewa maso Yamma bakwai suke ƙarƙashin jam’iyya guda.

Kara karanta wannan

APC ta yi wa gwamnan Osun barazana ana dab da zabe

Jam’iyyar ta ce wannan dama ce ta musamman wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma ci gaba da gina nasarorin da ta samu a yankin.

Uba Sani ya sha yabo daga APC a Arewa
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Uba Sani.
Source: Facebook

An yabawa Gwamna Uba Sani

Shugabannin shiyyar sun yabawa Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa bai wa sakatariyar APC ta shiyyar motar aiki domin sauƙaƙa gudanar da ayyukanta.

Sun ce gudummawar ta nuna jajircewar gwamnan wajen bunƙasa APC da kuma tabbatar da ingantaccen gudanar da harkokin jam’iyyar a Arewa maso Yamma, cewar Daily Post.

Jam’iyyar ta kuma yaba wa gwamnonin APC na yankin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ministoci da sauran masu riƙe da muƙamai.

APC ta buƙace su su ci gaba da mara wa jam’iyyar da gwamnatin Shugaba Tinubu baya yayin da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi.

An yaba wa ayyukan alheri na Tinubu

Mun ba ku labarin cewa jigo a APC Kano, Iliyasu Musa Kwankwaso, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa kokarin da yake yi a jihar.

Kwankwaso ya ce hakan zai ƙarfafa tattalin arzikin Arewa, ya bunƙasa kasuwanci, sannan ya buƙaci al'umma su rika yaba ayyukansa.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya ce an saki kusan kashi 60 cikin ɗari na kuɗin ayyuka a Kano Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.