Zakaran da Allah Ya Nufa da Cara: Jariri Sabon Haihuwa da aka Sace Ya Kubuta
- Rundunar ’yan sandan Benue ta tabbatar da ceto wani jariri da aka yi zargin sace shi bayan haihuwarsa a wani asibiti da ke jihar
- An ceto jaririn a safiyar Alhamis, 13 ga watan Agusta, 2026 yayin da ’yan sanda suka tabbatar da kama wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin
- An gano halin da mahaifiyar jaririn ke ciki bayan Allah Ya taimaka an gano jaririn da ta haifa bayan ta sha nakuda da shiga takaici bayan sace shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Benue – Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta tabbatar da ceto wani jariri da aka yi zargin sace shi sa’o’i kadan bayan haihuwarsa a wani asibiti da ke karamar hukumar Gboko ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Peter Aondona, ne ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Makurdi ranar Alhamis 13 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Aondona ya ce an fara kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na A Division da ke Gboko, kafin daga bisani a mika shi ga sashen binciken manyan laifuka (CID) domin gudanar da cikakken bincike.
An gano jaririn da aka sace
The Sun Nigeria ta ruwaito Aondana ya ce an gano jaririn ne a safiyar Alhamis, kuma a halin yanzu yana hannun ’yan sanda, yayin da aka kama wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin.
Ya ce:
“Za a sanar da adadin wadanda aka kama daga baya, amma zan iya tabbatar da cewa an kama wasu mutane kuma an gano jaririn."
An haifi jaririn ne a safiyar ranar 11 ga watan Agusta, 2026 inda rahotanni suka ce an dauke shi daga wajen mahaifiyarsa jim kadan bayan haihuwarsa.
Yadda aka sace jariri a Benue
Rahotanni sun ce jaririn bai yi kuka nan take bayan haihuwarsa ba, lamarin da ya sa wata ma’aikaciyar jinya da ke bakin aiki ta shiga tsakani domin taimaka masa har aka samu nasarar daidaita yanayinsa.
Sai dai majiyoyi sun ce wata matar da ba a san ko wace ce ba ta je wajen mahaifiyar, inda ta gabatar da kanta a matsayin ma’aikaciyar jinya tare da neman sake duba jaririn.

Source: Twitter
Rahotanni sun ce mahaifiyar ta mika mata jaririn, sannan matar ta nufi dakin haihuwa da shi. Kakarsa ta bi ta, amma an ce matar ta bukace ta da ta tsaya a waje.
Daga bisani aka gano cewa jaririn ya bace, yayin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka musanta cewa sun dauke shi, tare da cewa matar ba ma’aikaciyar asibitin ba ce.
An sace jariri 'dan wata 1
A baya, mun wallafa cewa rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta bayyana cafke wata mata mai suna Blessing bisa zargin shiga har cikin gida tare da sace wani jariri dan wata daya.
Mahaifiyar jaririn ce ta garzaya ofishin ‘yan sandan Elere inda ta ce tana barci da sanyin safiyar Asabar lokacin da matar ta lallaba ta dauke mata jariri Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar.
SP Benjamin Hundeyin ya ce tuni aka kama matar a Agbotikuyo da ke Agege kuma ta shaidawa mutane cewa 'danta ne, lamarin da ya jawo kwanciyar hankali ga mahaifiyar jaririn.
Asali: Legit.ng

