Shugaban Majalisa da Wasu Wakilai 2 Sun Sha 'Kasa a Zaben Tsaida Gwanin APC a Nassarawa
- Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa, Danladi Jatau, ya sha kaye a takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya a zaben fitar da gwani na APC
- Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu masu ci sun rasa tikitin komawa takara a zabukan fitar da gwani da aka gudanar a jihar gabanin zaben 2027
- Kwamitin APC ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana, adalci da gaskiya a dukkannin kananan hukumomi 13 na Nasarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Nasarawa - Kakakin Majalisar Dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Danladi Jatau, ya rasa damar tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Keffi/Karu/Kokona bayan da ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.
Rt. Hon. Danladi Jatau ya samu kuri’u 5,873 ne kacal, yayin da abokin takararsa, Hon. Daniel Ogazi, ya lashe zaben da kuri’u 13,083.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ce haka kuma wasu ‘yan majalisar wakilai biyu masu ci sun rasa tikitin komawa takara bayan kammala zabukan fitar da gwani a cikin lumana a mazabunsu daban-daban.
'Yan Majalisa a APC sun rasa tikiti
Arise News ta wallafa cewa ‘yan majalisar da abin ya shafa sun hada da Mohammed Abdulmumini Ari mai wakiltar Nasarawa/Toto da kuma Jeremiah Umaru mai wakiltar Akwanga/Nasarawa Eggon/Wamba.
Da yake sanar da sakamakon zaben a Lafia, shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC na Majalisar Tarayya a Nasarawa, Musa Shuaibu Guri, ya ce an gudanar da zaben bisa tsarin kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin zabe da kuma ka’idojin jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci a dukkan kananan hukumomi 13 na jihar, saboda haka babu wanda aka zalunta.
Wadanda suka yi nasara a zabukan APC
Daga cikin wadanda suka samu tikitin takarar APC akwai Mohammed Al-Bashir na mazabar Nasarawa/Toto, Daniel Ogazi na Keffi/Karu/Kokona, da Tony Bala Shammah na Akwanga/Nasarawa Eggon/Wamba.

Source: Facebook
Haka kuma Mohammed Al-Makura ya zama dan takarar APC na mazabar Lafia/Obi bayan da abokin hamayyarsa Isaac Kigbu ya janye daga takarar tun ranar Asabar.
Sai dai Guri ya bayyana cewa har yanzu ana tattara sakamakon mazabar Awe/Doma/Keana, inda za a sanar da shi nan gaba.
A cewarsa:
“Mohammed Al-Bashir ya samu kuri’u 31,796 yayin da Ari Abdulmumini Mohammed ya samu kuri’u 9,039, saboda haka an ayyana Al-Bashir a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na mazabar Nasarawa/Toto.”
Ya kara da cewa Tony Bala Shammah ya samu kuri’u 38,333, yayin da Jeremiah Umaru ya samu kuri’u 4,061 a mazabar Akwanga/Wamba/Nasarawa Eggon.
Game da mazabar Keffi/Karu/Kokona kuwa, Guri ya ce Daniel Ogazi ne ya yi nasara da kuri’u 13,083, yayin da Danladi Jatau ya samu kuri’u 5,873, sannan Abdulaziz Danladi ya samu kuri’u 1,067.
Kwamitin APC ya yi kira ga dukkannin masu neman takara, wadanda suka yi nasara da wadanda suka fadi, da su hada kai domin karfafa jam’iyyar gabanin zaben 2027.

Kara karanta wannan
Yusuf Buhari ya san matsayarsa bayan kammala zaben fitar da gwani na APC a Katsina
Sanatan APC ya fice daga jam'iyya
A wani labarin, mun wallafa cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rasa daya daga cikin sanatocin da take da su a Majalisar dattawa wadanda suka fito daga jihar Kebbi.
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar dattawa, Garba Maidoki, ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar APC ba tare da bata lokaci ba ta cikin wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Mayu, 2026.
Murabus din nasa daga APC na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben fitar da gwani na masu neman takarar sanata a karkashin inuwar jam'iyyar mai mulki, ya aika wasikar ga uwar jam'iyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

