Shugaba a Kwankwasiyya Ya Gana da Abba Kabir, Yana Shirin Shiga APC

Shugaba a Kwankwasiyya Ya Gana da Abba Kabir, Yana Shirin Shiga APC

  • Shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano, Alhaji Abdulaziz Gidanruwa, ya ziyarci Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Gidanruwa, wanda ake bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu ɗaukar nauyin NDC da ƙungiyar Kwankwasiyya a Nassarawa,
  • Ziyarar ta ƙara haifar da hasashen sauye-sauyen siyasa a Kano yayin da jam'iyyu ke fara shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Alhaji Abdulaziz Gidanruwa, ya ziyarci Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin da ake sa ran zai fice daga jam'iyyar NDC zuwa APC.

Gidanruwa na daga cikin mutanen da ake bayyana cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen ɗaukar nauyin NDC da kuma ƙungiyar Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Nassarawa.

Kara karanta wannan

Dan takarar NDC: 'Abin da ya sa Najeriya ke bukatar Obi da Kwankwaso'

Abba Kabir Yusuf da Dan Kwankwasiyya
Dan Kwankwasiyya, Abdulaziz Gidanruwa tare da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a wani sako da hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ibrahim Adam ya wallafa a Facebook.

Dan Kwankwasiyya ya ziyarci Abba

Rahoton ziyarar ya fito ne daga mai ba Gwamnan Kano shawara na musamman kan kafafen sada zumunta, Ibrahim Adam.

Ziyarar Gidanruwa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na zuwa ne yayin da ake ƙara samun sauye-sauyen siyasa a jihar Kano gabanin zaɓen 2027.

Idan sauyin ya tabbata, hakan na iya zama wani sabon sauyi a tsarin siyasar Kano, musamman ganin matsayin da Gidanruwa ke da shi a cikin Kwankwasiyya a Nassarawa.

Magoya baya sun yi martani

Wasu daga cikin mutanen da suka yi martani kan lamarin sun bayyana farin cikinsu da matakin da Gidanruwa ya ɗauka.

Mustapha A Hassan Sa'id ya ce sauyin ya samo asali ne daga irin ayyukan raya kasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake gudanarwa, musamman wajen tallafa wa matasa da ayyukan ci gaba.

Kara karanta wannan

APC ta wawushe magoyan PDP da ADC, Gwamna Radda ya karbi masu sauya sheka

Ya ce:

"Wannan ya samo asali ne daga irin ci gaban da Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf yake samarwa, musamman wajen tallafa wa matasa da ayyukan ci gaba."

Aminu Ogan Biye shi ma ya taya shugaban murna, yayin da Abdulkarim Bilal Mahmud ya ce ana sa ran wasu mutane da dama za su bi sahun Gidanruwa.

Ya ce:

"Mutane da yawa suna nan tafe in sha Allah, amma har yanzu ba ku ba ni filina ba."
Yan Kwankwasiyya a wajen taro
Yadda 'yan Kwankwasiyya suka taru a gidan Rabiu Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Wasu sun yi tsokaci kan sauyin

Ummalkhair Kabawa ta bayyana ra'ayinta kan siyasar, tana mai cewa lokaci ne zai tabbatar da waɗanda suke da ƙaunar shugabanni da gaske.

Isa Aliyu kuwa ya ce ko da wasu daga cikin Kwankwasiyya sun fice, hakan ba zai girgiza ƙungiyar ba.

Ya ce:

"Kwankwasiyya, ikon Allah, kowa zai fita, ba za mu girgiza ba."

Kwankwaso ya soki Sheikh Jingir

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna damuwa kan wasu kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir da ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan

"Za ka sha kaye"; Dan takarar ADC ya yi wa Gwamna Abba barazana kan zaben 2027

Ya bayyana cewa kalaman da ke iya haifar da rarrabuwar kawuna da rashin haɗin kai ya kamata a yi Allah-wadai da su musamman a wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya.

Kwankwaso ya kuma jaddada cewa bai kamata a bar kalaman da za su iya raba kan al'umma su samu karɓuwa ba, musamman idan sun fito daga wani malamin addini mai tasiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng