Matashi Mai Basira Ya Kirkiri Manhajar Inganta Harkar Noman Kaji a Katsina
- Abubakar Sadiq Abbas ya kirkiro wata manhaja da ake kira PoultryPro da za ta canza rayuwar manoma da makiyaya
- Matashin mai fasaha ya ce da manhajarsu, manomi zai iya ajiye bayanai kuma ya iya hango yanayin kasuwa nan gaba
- Da PoultryPro, Malam Abu Abbas ya ce masu gidajen gona za su yi lissafin kudin shiga, riba da sauran ayyuka kula da aikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina - Abubakar Sadiq Abbas kwararre ne a fasahar kirkirar manhajojin komfuta da yake zamanantar da kiwo a garin Katsina.
Malam Abubakar Sadiq Abbas ya karanci ilmin na’ura mai kwakwalwa kuma yanzu ya shigar da wannan wajen sha’anin kiwonsa.

Source: UGC
Matashi ya kirkiro manhajar PoultryPro domin gonaki
Rahoto na musamman da Daily Trust ta fitar ya nuna yadda matashin ya kirkiri manhajar da za ta kawo wa masu gidan gona sauyi.
Kafin ya kirkiri manhaja mai suna PoultryPro, Abubakar Sadiq Abbas ya shafe shekaru takwas a matsayin manajan gidan gonar kaji.
A hirar da aka yi da shi, matashin ya ce ilmin da ya samu a jami’a a fannonin fasaha da gudunar da kasuwanci suka taimaka masa.
Amfanin PoultryPro a gidajen gona
Manhajar da ya kirkira za ta zamantar da kula da gonaki tun daga wajen kyankyasar kwai, bada abinci da lura da adadin kaji a gona.
Da wannan manhaja, manomi zai iya magance matsalar mace-macen dabbobi, ya bada magani kuma a yi wa dabbobin nasa rigakafi.
Amfanin bai tsaya a nan ba, PoultryPro yana kula da lissafin kudi da cinikin da ake yi a gidajen gona.
Abu Abbas ya ce:
“Manoma za su iya ganin yadda abubuwa suke tafiya, cin abinci, kokarin tsuntsunaye, kashe-kashen dukiya da kuma kudin shiga da sauran alkaluma, sannan ya taimaka masu su fahimci yadda gonarsu ta ke tafiya, maimakon a bar su cikin kila-wa-kala.
“PoultryPro ya kuma hada da kirkirarriyar fasaha ta AI. Manufar ita ce wannan AI ta iya nazarin tarihi da bayanin gona, ta hango yanayin da ba a tunani kuma ta bada haske, ta yi hasashe tare da yi wa manoma gargadin da zai taimaka masu wajen daukar matakai."

Source: Getty Images
Da PoultryPro, makiyayi zai samu saukin fahimtar yadda za a samu riba kuma jama’a za su iya sauke manhajar daga shafin yanar gizo a na’urorin hannu.
Sauyi yana shigowa masu kiwon kaji
Malam Abubakar Abbas wanda yanzu yake digirinsa na PhD ya ce ya yi tunanin wannan aiki ne tun da ya fara kiwon kaji a shekarar 2017.
A lokacin ana tattara duk wasu bayanai ne a gargajiyance ko akalla ba tare da tsari ba, don haka ya iya ganin irin wahalar da ake sha a gona.
A cewarsa, kowane aiki irin wannan bai rasa ‘yan kalubale, daga cikin wadanda yake fuskanta har da sha’anin kudi wajen kirkirar fasahar.
Matsalolin kiwon kaji a Najeriya
An taba samun rahoton yadda kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya (PAN) ta koka da ruwan da bankuna ke karba wanda yake karya kasuwancinsu.
Shugaban kungiyar, Dr. Ayoola Oduntan, ya bayyana cewa tsadar kudin ruwa, tashin dalar Amurka, da tsadar abincin kaji na gurgunta harkar kiwo.
Hakazalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakai wajen rage kudin ruwan banki da kuma dakile shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya.
Asali: Legit.ng

