'Yan Najeriya da Dab da Rasa Damar da Aka Bude Musu kan Batun Kafa Yan Sandan Jihohi

'Yan Najeriya da Dab da Rasa Damar da Aka Bude Musu kan Batun Kafa Yan Sandan Jihohi

  • Fadar Shugaban Kasa ta shirya rufe karbar ra'ayoyin yan Najeriya kan kudurin kafa yan sandan jihohi a yammacin Alhamis, 13 ga Agusta, 2026
  • Kudirin na neman samar da tsarin kafa ‘yan sandan jihohi da nufin magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya
  • Femi Gbajabiamila ya ce ana bukatar ra’ayoyin ‘yan Najeriya kan yadda za a kare tsarin daga katsalandan na siyasa da take hakkin jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fadar Shugaban Kasa ta sanya karfe 5 na yammacin Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, a matsayin wa’adin karshe da ‘yan Najeriya za su gabatar da ra’ayoyinsu kan kudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa kuma Shugaban Kwamitin da aka kafa kan kudirin dokar, Femi Gbajabiamila, ne ya sanar da wa’adin ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Hukumar alhazai ta sanar da kuɗin kujerar hajjin shekarar 2027 a jihar Kano

Gbaja.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

Ya ce an bude damar da jama’a za su mika ra'syoyinsi ne domin shigar da kwarewa da gogewar ‘yan Najeriya cikin kudirin dokar, musamman kan batun katsalandan na yan siyasa, cewar rahoton Punch.

Ana so yan Najeriya su mika shawarwari

Gbajabiamila ya bukaci ‘yan Najeriya da su gabatar da shawarwarinsu kafin wa’adin ya cika, yana mai jaddada cewa wannan tuntuba ba za ta kwace ikon Majalisar Tarayya na yin doka ba.

Ya ce Majalisar Tarayya za ta ci gaba da kasancewa da ikon duba kudirin, gyara shi, kin amincewa da shi ko kuma amincewa da shi idan aka gabatar mata da shi daga bisani.

Ya kuma bukaci jama’a da su ba da shawarwari kan yadda za a kare ‘yan sandan jihohi daga katsalandan na siyasa, da kuma yadda ‘yan sandan tarayya da na jihohi za su rika musayar bayanan sirri a tsakani.

Gwamnatin tarayya za ta bi tsarin doka

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun jajubo rigima da jam'iyyar, an ba su wa'adi su gyara alaka da ita

A rahoton Tribune Nigeria, Gbajabiamila ya ce:

"An dade ana kallon wannan muhawara a matsayin zabi tsakanin ingantaccen tsaron cikin gida da kuma kare jama’a daga cin zarafin siyasa. Najeriya na bukatar duka biyun.”
“Za mu iya kusantar da aikin ‘yan sanda ga jama’a tare da samar da ingantattun ka’idojin kasa, sa ido mai zaman kansa da kuma tsauraran matakan kariya ga kowane dan kasa.
"Lokacin gyara tsarin ‘yan sanda a Najeriya ya yi, kuma dole ne mu kammala wannan aiki.”
Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock, Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Gbajabiamila ya jaddada cewa tsarin dole ne ya kare kowa ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da yake goyon baya ba.

Gbajabiamila ya bayyana cewa akalla majalisun dokokin jihohi 24 daga cikin 36 ne dole su amince da gyaran kudin tsarin mulki don kafa yan sandan jihohi kafin a iya mika shi ga Shugaban Kasa domin sanya hannu.

Najerirya ta yi nazari kan kasashe 3

Kun ji cewa Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Olatunji Disu, ya ce kwamitin da ya tsara tsarin 'yan sandan jihohi ya yi nazarin yadda ake gudanar da su a kasashe waje uku.

Disu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na da yakinin cewa kafa 'yan sandan jihohi zai bada gudunmawa wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262