Bauchi: Shugaban Masu Rinjaye Ya Yi Murabus Ya Bar Majalisa, an Ji Dalili

Bauchi: Shugaban Masu Rinjaye Ya Yi Murabus Ya Bar Majalisa, an Ji Dalili

  • Saleh Hodi ya yi murabus daga Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da kuma matsayinsa na shugaban masu rinjaye
  • Dan majalisar ya kasance wakilin mazabar Disina ta jihar Bauchi a majalisar tun bayan zabensa na farko a shekarar 2019
  • Bayan murabus dinsa, jam'iyyar APM ta tsayar da Auwal Yana a matsayin sabon shugaban masu rinjaye na majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Saleh Hodi, shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, ya yi murabus daga kujerarsa ta wakiltar mazabar Disina domin ya tsaya takarar zaben shugaban karamar hukumar Shira da ke tafe a jihar.

Saleh Hodi da ke wakiltar mazabar Disina, ya kasance dan majalisar tun bayan da aka fara zaben sa a shekarar 2019.

Saleh Hodi ya yi murabus
Hon. Saleh Hodi, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Bauchi Hoto: Abbati Hamza Beli
Source: Facebook

Kakakin majalisar, Abubakar Sulaiman, ne ya sanar da murabus din Hodi yayin zaman majalisar na ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026 a Bauchi, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Hanyar da APC za ta bi don lashe zaben gwamnan Osun'

Sulaiman ya ce majalisar ta karbi wasikar Hodi wadda ya sanar da ita a hukumance cewa ya yi murabus daga kujerarsa ta wakiltar mazabar Disina.

Dalilin murabus din dan majalisar

Kakakin majalisar ya ce murabus din ya biyo bayan shawarar Allied People’s Movement (APM) na tsayar da Hodi a matsayin dan takararta a zaben shugaban karamar hukumar Shira.

“Majalisar ta karbi wasika daga Honourable Saleh Hodi, inda ya sanar da mu a hukumance cewa ya yi murabus daga mukaminsa na dan majalisar da ke wakiltar mazabar Disina."
“Murabus din ya biyo bayan shawarar Allied People’s Movement na tsayar da shi a matsayin dan takararta a zaben shugaban karamar hukumar Shira.” In ji shi

Hon. Saleh Hodi ya yi bankwana

A jawabinsa na bankwana, Hodi ya gode wa kakakin majalisar da sauran ’yan majalisar bisa hadin kai, shawarwari da goyon bayan da suka ba shi a tsawon wa’adinsa.

Ya kuma gode wa al’ummar mazabar Disina da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar bisa amincewar da suka nuna masa da kuma goyon bayan da suka ba shi har ya zama dan takarar jam’iyyar na shugabancin karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Atiku ya yi gargadi mai zafi ga INEC, Tinubu kan zaben Osun

“Kwarewata a wannan majalisa abin tunawa ce, kuma ina godiya da damar da aka ba ni na yi wa al’ummata hidima tare da ba da gudummawa wajen ci gaban Jihar Bauchi."
“Ina godiya da amincewar da mutanen Disina, masu ruwa da tsaki a Shira da Mai Girma Gwamna Bala Mohammed suka nuna mini. Idan aka zabe ni a matsayin shugaban karamar hukumar, zan yi aiki tukuru domin wuce abin da kuke tsammani daga gare ni.” In ji shi.

APM ta nada sabon shugaban masu rinjaye

Bayan murabus din Hodi, kakakin majalisar ya sanar da ’yan majalisar cewa APM ta tsayar da Auwal Yana, wanda ke wakiltar mazabar, a matsayin sabon shugaban masu rinjaye.

A cewar kakakin majalisar, nadin ya biyo bayan wani taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka gudanar domin maye gurbin Hodi.

Shugaban masu rinjaye na Bauchi ya yi murabus
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An ba Jonathan sarauta a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa masarautar Bauchi ta ba tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sarautar gargajiya na girma.

Masarautar ta ba Jonathan sarautar Jigon Bauchi saboda gudunmawarsa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng